Masu ruwa da tsaki na APC a Dawakin Tofa sun tattauna hanyar kawo cigaban ƙaramar hukumar

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa sun gudanar da taro na musamman da yammacin ranar Litinin, domin tattauna muhimman batutuwa da za su taimaka wajen bunƙasa cigaba da hadin kai a ƙaramar hukumar.

Taron wanda ya samu halartar manyan jagorori da jiga-jigan jam’iyyar daga matakai daban-daban.

Daga cikin mahalarta akwai babban daraktan yada labarai na Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Sanusi Bature D-Tofa.

Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Adamu Shehu Bello Danmaliki,tsohon ɗan takarar majalisar tarayya a jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Injiniya Abba Ganduje da kuma ɗan majalisar Jihar Kano mai wakiltar Dawakin Tofa, Alhaji Sale Marke.

Haka kuma taron ya samu halartar tsohon ɗan takarar majalisar jihar Dawakin Tofa a zaɓen 2023, Hon. Ahmad Muhammad (Speaker), mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Abdullahi Magaji Aliyu Kosasshe ,House Leader na Dawakin Tofa, Hon. Auwalu Dahiru Dambazau tare da sauran manyan jagororin jam’iyyar.

Masu jawabi a taron sun jaddada buƙatar haɗin kai, fahimtar juna da kuma tsara dabarun da za su kawo cigaba mai ɗorewa ga al’ummar Dawakin Tofa. A ƙarshe, mahalarta sun yi addu’ar Allah maɗaukakin sarki ya tabbatar da nasara da zaman lafiya a yankin.

By ukarofi