Trump ya tura wa Nijeriya sojoji don magance matsalar tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Donald Trump, ta tura wani ƙaramin rukunin sojoji zuwa Nijeriya.

Babban Janar da ke kula da rundunar sojin Amurka a Afirka (AFRICOM), Dagvin R.M. Anderson ya bayyana a ranar Talata.

Wannan shi ne karon farko da aka tabbatar da kasancewar sojojin Amurka a Nijeriya tun bayan da Washington ta kai hare-haren sama a ranar Kirsimeti.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin kai hare-haren sama kan abin da ya bayyana a matsayin wuraren da ’yan kungiyar Islamic State ke amfani da su a Nijeriya a watan Disamba, inda ya ce akwai yiwuwar ƙarin matakan soja na Amurka nan gaba.

Babban janar ɗin ya ce an tura rukunin sojojin ne bayan da ƙasashen biyu suka amince cewa akwai buƙatar ƙara ƙoƙari wajen yaki da barazanar ta’addanci a yankin Yammacin Afirka.

“Hakan ya haifar da ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashenmu, ciki har da tura ƙaramin rukunin sojojin Amurka da ke kawo wasu ƙwarewa ta musamman daga Amurka,” inji Janar Dagvin.

A nasa ɓangaren Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa ya shaida wa manema labarai cewa Amurka ta tura wata ƙaramar tawagar sojoji wadda tuni ta isa ƙasar don taimaka wa wajen magance matsalar tsaro da ke addabar Nijeriya.

Ya ce, sojojin na Amurka za su bai wa na Nijeriya horo domin su iya tunkarar ʼyan bindiga a yayin fafatawa.

Wani tsohon jami’in Amurka ya ce rukunin sojojin na Amurka na taka muhimmiyar rawa wajen tattara bayanan sirri da kuma taimaka wa sojojin Nijeriya wajen kai hare-hare akan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.

By Babaji