
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta ce jami’anta sun yi nasar cafke wani ɗan kasuwa mai shekaru 62 mazaunin Lagas mai suna Nwabueze Nicholas Izueke a Filin Jiragen Sama na Mallam Aminu Kano a lokacin da yake shirin tafiya kasar Chana ɗauke da wasu ƙullin hodar iblis guda 95.
An kama mutumin ne a jiya Asabar yayin tantance fasinjojin da za su tafi Chana ta Addis Ababa cikin jirgin Ethiopian Airlines, kamar yadda Daraktan yaɗa labaran hukumar, Femi Babafemi ya bayyana a wata takarda.
A cewarsa, bayan an yi masa gwajin jiki, an tabbatar da ya haɗiye miyagun kwayoyi, inda nan take aka tsare shi tare da sanya shi ƙarƙashin kulawar likitoci.
Yayin da yake ƙarƙashin kulawa, dillalin ya bayyana cewa harkar sayar da kayan sawa da na gyaran motoci yake yi a Lagas, ya fitar da ƙunshi 95 na hodar iblis daga ɓangarori bakwai na kayansa.
A bayaninsa, ya ce ya shiga harkar ne domin tara kuɗin kammala ginin gidansa na ƙauye da yake ginawa a Iwollo, Jihar Inugu.
