IPOB ta soke umarnin zaman gida bayan Nnamdi Kanu ya umarci haka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB), ta sanar da soke gaba ɗaya umarnin zama a gida a ranakun Litinin a duk faɗin shiyyar Kudu maso Gabas, daga ranar 9 ga Fabrairu, 2026.

Kakakin IPOB, Emma Powerful ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, inda ya ce umarnin ya fito ne kai tsaye daga tsararren shugaban ƙungiyar, wato Nnamdi Kanu.

Emma Powerful ya ce babu wani dalili ko hujja da zai sa mutane su zauna a gida a ranakun Litinin, yayin da kasuwanni, makarantu, ofisoshi, ayyukan sufuri da dukka. harkokin tattalin arziƙi suke cigaba da aiki kamar yadda ya kamata a halin zamantakewa.

Ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan umarnin Kanu ne na tabbatar da cewa yara su koma makaranta a kowace Litinin, kuma al’umma su gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsoro, barazana ko tsangwama ba daga gare su.

Umarnin zama a gida da IPOB ta ayyana tun a Agustan 2021 a matsayin hanyar nuna rashin amincewa da tsare Kanu ya shafi kasuwanni, makarantu, bankuna da ofisoshi a lokacin.

Sannan, matakin soke zaman a gida ya nuna sauyin yanayi a yankin, inda al’umma ke fatan gudanar da harkokinsu cikin lumana da tsaro ba tare da fargabar wani abi ka iya haifar musu da tsaiko ba.

By Babaji