Shettima zai jagoranci zaman Majalisar Tattali a ranar Litinin

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya za ta gudanar da taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) na tsawon kwanaki biyu daga ranar 9 ga Fabarairu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja domin ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziƙi da bunƙasa cigaba mai amfani ga dukkan jihohin Nijeriya.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne zai jagoranci taron, wanda zai haɗa gwamnonin jihohi, manyan masu ruwa da tsaki na ƙasa, abokan cigaba da shugabannin ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu.

Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi ce ta shirya taron, wanda za a mayar da hankali akan daidaita harkokin kuɗi, zuba jari, da daidaita tsare-tsaren tattalin arziki tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi domin cimma manufar Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Tinubu

Haka kuma akwai yiwuwar Shugaba Tinubu ya halarci taron a matsayin baƙo na musamman, yayin da ake sa ran taron zai taimaka wajen tsara manyan manufofin tattalin arziki da jihohi za su bi bisa la’akari da dogon shirin tattalin arziƙin Gwamnatin Tarayya.

NEC, wadda ke ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tattalin arzikin ƙasa, a baya ta amince da kafa Hukumar Bunƙasa Auduga, Tufafi da Kayan Sawa, da tsare-tsaren bunƙasa noma da kiwon dabbobi, tare da Shirin Green Imperative, waɗanda ake sa ran za su samar da darajar tattalin arziƙi har Dala biliyan 90 nan da 2035.

By Babaji