DSS ta yi gargaɗin aukuwar wani hari a Kwara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, reshen jihar Kwara, ta aike wa Rundunar ‘yan sandan jihar saƙon yiwuwar samun wani hari a Ƙauyen Gbabe na Ƙaramar Hukumar Baruten.

Wannan gargaɗi na zuwa ne kwanaki kaɗan da ‘yan ta’adda suka ƙaddamar da wani mummunan hari a Ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Hukumar Kaiama, inda suka halaka mutane da dama.

A samu wani kwafin takardar ankararwar daga Daraktan DSS, J.S. Adams da ke ɗauke da kwanan wata kamar haka: 5 ga Fabrairu, 2026, inda a ciki aka nufaci Kwamishinan ‘yan sandan yayin da ake tsaka da ƙaruwar taɓarɓarewar lamuran tsaro a arewacin jihar.

A cikin wasiƙar, hukumar ta yi gargaɗin cewa an gano zirga-zirgar wasu mayaƙan ƙungiyar Mamuda a yankin Kiyoru da ke Gundumar Gwanara.

Haka kuma, ta yi tsokaci akan ayyukan ta’addanci da suka faru a baya a yankin Kainji Lake National Park, lamarin da ya sa ta buƙacin jama’a da su kasance masu sanya ido a yankunansu.

Tuni dai DSS ta buƙaci ‘yan sandan da su gaggauta amfani da tsarin leƙen asiri wajen ɗaukar matakan da suka dace domin shawo kan al’amarin.

A ‘yan watannin nan al’amarin taɓarɓarewar tsaro a sassan Nijeriya ya ƙaru duk da ayyana dokar ta-ɓaci a fannin da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

By Babaji