El-Rufa’i zai je ofishin EFCC bayan yunƙurin kama shi a filin jiragen saman Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An samu hatsaniya a Filin Jiragen Sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja a yau Alhamis bayan da aka zargi jami’an tsaro da yunƙurin kama tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i jim-kaɗan da dawowarsa Nijeriya daga Cairon kasar Masar.

Mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ya bayyana hakan ta kafafen sada zumunta, wanda a cewarsa, jami’an tsaro sun tare El-Rufa’i ne a daidai lokacin da ya iso Nijeriya.

Ya yi zargin cewa, jami’an sun yi yunƙurin tafiya da tsohon gwamnan zuwa ofishinsu a lokacin. Saidai El-Rufa’i ya ƙi bada haɗin kai akan hakan inda ya kafa hujja da rashin takardar izinin kamu daga ɓangaren jami’an a matsayin dalilinsa na tirjewa.

Mataimakin ya ƙara da cewa, a yayin gamuwar, jami’an tsaron sun kuma ƙwace fasfon El-Rufa’i.

Saidai, a yayin haɗa wannan rahoto ba a iya tantance ko Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) ko ta Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ce ke da alhakin yunƙurin kame ba.

A nasa jawabin, Lauyan El-Rufa’i, Ubong Esop Akpan ya bayyana yunƙurin kamen a matsayin tauye wa tsohon gwamnan ‘yancin da doka ta ba shi da bijire wa hukuncin doka.

Ya bayyana cewa, tun a watan Disambar 2025 ne EFCC ta aike wa El-Rufa’i saƙon gayyata ta musamman a lokacin da yake ƙasar wajen, wanda ya hana shi zuwa a nan take.

A cewarsa, tawagar shari’arsa tun a Disambar suka shaida wa EFCC cewa El-Rufa’i zai amsa gayyatarsu da zarar ya dawo gida Nijeriya.

Lauyan ya ƙara da cewa, sun sanar da hukumar cewa zai je wajenta da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026.

By Babaji