Shirin Operation Savannah Shield da kisan gilla a Jihar Kwara

Spread the love

Bayan da rahotanni suka bayyana yadda ’yan ta’adda suka hallaka mutane da dama a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura bataliyar sojoji ta musamman zuwa yankin domin daƙile lamarin.

Aikin, wanda aka sanya wa suna Operation Savannah Shield, ana sa ran zai kawo ƙarshen hare-haren ta’addanci da suka addabi jihohin Kwara, Katsina da Benuwe, inda aka rasa rayukan ɗaruruwan bayin Allah marasa laifi.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 70 aka kashe a hare-haren da aka kai kan al’ummomin Woro da Nuku a Kaiama a daren Talata.

A wani harin daban kuma, a unguwar Abande da ke Mbaikyor Ward, Turan a ƙaramar hukumar Kwande ta jihar Benuwe, ‘yan bindiga sun yi mummunan ta’adi inda aka ce sun hallaka mutane da dama.

Cikin gaggawa, Shugaba Tinubu ya sanar da kafa sabuwar tawagar soja domin jagorantar Operation Savannah Shield da nufin murƙushe waɗannan ‘yan ta’adda da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, an ce shugaban ya yi Allah-wadai da harin, yana mai bayyana maharan a matsayin marasa imani da tausayi, saboda kai hari kan al’umma marasa ƙarfi.

Shugaban ya nuna takaici kan yadda maharan suka hallaka wasu daga cikin mutanen da suka ƙi amincewa da wani ra’ayi na addini mai tsattsauran ra’ayi da ke fifita tashin hankali a kan zaman lafiya. Ya yaba wa al’ummar da suka tsaya tsayin daka wajen ƙin amincewa da irin wannan aƙida mai hatsari.

Hakazalika, shugaban ya buƙaci haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi domin tallafawa al’ummar da abin ya shafa tare da tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan ta’asa ba su tsira ba. Ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan wazanda suka rasu tare da jajanta wa iyalansu da gwamnatin jihar Kwara.

A ɓangaren ’yan sanda kuwa, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, shi ma ya bayar da umarnin tura jami’an musamman da na leƙen asiri zuwa Kaiama da kewayenta. Kakakin rundunar, ACP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta yi Allah-wadai da harin tare da jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da gwamnatin Kwara.

Rundunar ta ce, an fara farautar waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, tare da yin alƙawarin cewa za a kamo su a gurfanar da su gaban kotu. Haka kuma ta roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai domin taimaka wa bincike.

Abin takaici, harin na Kaiama ya zo da sabon salo mai hatsari, inda maharan suka mayar da hankali kan tilasta wa mutane karɓar wata aƙida mai tsauri, saɓanin yadda a baya aka fi samun satar mutane domin neman kuɗin fansa. Wannan sabon salo na nuna sauyin dabarun ‘yan ta’adda zuwa wata manufa mai zurfi ta aƙida, wanda ke ƙara jefa al’umma cikin barazana.

A wannan mahallin ne ya dace a yaba wa matakin gaggawa da Shugaba Tinubu ya ɗauka na tura sojoji domin murƙushe ‘yan ta’adda. Haka kuma, ana fatan haɗin gwiwar jami’an tsaro, ciki har da rundunar ‘yan sanda da kuma goyon bayan abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Haƙƙin rayuwa da ’yancin gudanar da addini ba tare da tsangwama ba haƙƙi ne na asali da ba za a iya tauye shi ba. Don haka wajibi ne gwamnati ta tabbatar da kare waɗannan haƙƙoƙi tare da daƙile duk wani yunƙuri na tada fitina ko rusa zaman lafiya.

By ukarofi