Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ja hankalin khadi Mutawakil Mustapha Salis wanda aka naɗa da ya riƙa aiki da gaskiya, adalci, da tsoron Allah wajen gudanar da aikinsa.
Bikin rantsuwar, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin Jihar Katsina, ya samu halartar manyan baƙi daga ɓangarorin zartarwa, majalisa da shari’a na gwamnatin jiha, sarakunan gargajiya, malaman addinin Musulunci da ‘yan uwa da abokan arziki.
A wata takardar manema labarai, wacce Ibrahim Kaula Mohammed, babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Jihar Katsina ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya bayyana naɗin a matsayin wani mataki na ƙarfafa tsarin shari’ar Musulunci da inganta isar da adalci a faɗin jihar.
“Yau muna rantsar da sabon mai girma Alƙalin shari’a na kotun ɗaukaka ƙara ta shari’a ta Jihar Katsina. Wannan naɗi yana ƙarfafa tsarin shari’armu tare da inganta isar da adalci ga al’ummarmu,” in ji gwamnan.
Ya taya sabon Alƙalin murna tare da yaba wa hukumar ayyukan shari’a ta juha, kan gudanar da cikakken tsari na zaɓe bisa cancanta.
“Ofishinka babban nauyi ne. Dole ne ka riƙa tuna rantsuwar da ka yi kuma ta zama jagora ga ayyukanka. Dole ne ka yi adalci ba tare da tsoro ko son rai ba,” in ji shi.
Gwamna Raɗɗa ya tunatar da sabon Alƙalin cewa muƙamin sa amana ce mai girma a gaban Allah da al’umma. Yana mai kira gare shi da ya kasance mai bin adalci, gaskiya da koyarwar Musulunci.
“Ɓangaren shari’a shi ne mafaka ta ƙarshe ga talaka. Amincewar jama’a tana dogara ne kan gaskiya da ƙwazon ma’aikatan shari’a,” a cewar gwamna.
Malam Dikko Raɗɗa ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa ɓangaren shari’a tare da inganta haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori uku na gwamnati, domin tabbatar da zaman lafiya, tsari da adalci a jihar.
Daga cikin waɗanda suka halarta akwai sakataren gwamnatin jiha, Abdullahi Garba Faskari; Kwamishinar Shari’a kuma Babbar Lauyan Jiha, Barrista Fadila Muhammad Dikko; da babban Alƙalin shari’a na Jihar Katsina, tare da sauran manyan baƙi.
