Buƙatar cire shugaban INEC ba ta da nasaba da addini – Majalisar Shari’a

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar ƙoli ta Shari’a a Nijeriya (SCSN) ta sake fayyace dalilanta na kiran a cire tare da gurfanar da Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, tana mai jaddada cewa matsayinta bai samo asali daga bambancin addini ba, sai dai daga damuwa kan haɗin kan ƙasa, mutuncin hukumomi da kuma nauyin da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora.

A wata sanarwa da Sakatare Janar na majalisar, Nafi’u Baba Ahmad, ya aike wa manema labarai, majalisar ta ce an yi mata mummunar fahimta tare da karkatar da bayananta, lamarin da ya tilasta mata sake fito da cikakken bayani domin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a ƙasa.

Majalisar ta ce, ƙudurin da ta ɗauka a taronta na shekara-shekara kafin watan Ramadan, wanda ya gudana a ranar 28 ga Janairu, 2026, ya jawo ce-ce-ku-ce saboda buƙatar cire Shugaban INEC. 

Sai dai ta ce, wannan kira ba shi da alaƙa da addini ko ɓangaranci, illa dai abin da ta kira manyan damuwa kan tarihin halayya da ra’ayoyin da ake dangantawa da shugaban hukumar.

SCSN ta tunatar da cewa tun bayan samun ‘yancin kai a 1960, ba a taɓa ƙin amincewa da shugabannin hukumomin zaɓe bisa dalilin addini ba. Ta lissafo tsofaffin hukumomin zaɓe da suka haɗa da ECN, FEDECO, NEC da INEC, tana mai cewa an fi duba cancanta da halacci fiye da aƙidar shugabanni.

A cewarta, cikin mutane 13 da suka jagoranci hukumomin zaɓe a tarihin Nijeriya, mafi yawansu Kiristoci ne, yayin da Musulmi biyu ne kacal suka taɓa riƙe muƙamin — Farfesa Attahiru Jega da Farfesa Mahmood Yakubu — ba tare da wata adawa ta addini ba.

Majalisar ta ce, abin da ya bambanta lamarin Farfesa Amupitan shi ne wasu rubuce-rubuce da ake zargin ya wallafa a 2020, waɗanda suka sake fitowa fili. Ta ce takardun sun ƙunshi zarge-zarge da kalamai masu tayar da hankali kan Musulmi da tarihin Arewacin Nijeriya, ciki har da batun “kisan ƙare dangi na Kiristoci” da kuma alaƙanta matsalolin tsaro na yanzu da jihadin Shehu Usmanu ɗan Fodio na ƙarni na 19.

Majalisar ta ce, waɗannan zarge-zarge ba su da tushe a tarihi, kuma suna da haɗari ga zaman lafiya a ƙasa mai addinai da ƙabilu daban-daban kamar Nijeriya. Ta kuma ce an gabatar da waɗannan zarge-zarge ga wasu ƙasashen waje, lamarin da ka iya jefa Nijeriya cikin matsin lamba da katsalandan bisa hujjoji marasa tushe.

SCSN ta yi watsi da batun “kisan ƙare dangi na Kiristoci”, tana mai cewa rahotannin jinƙai da na ƙasa da ƙasa sun nuna cewa rikice-rikicen Arewa na da sarƙaƙiya, suna da nasaba da ta’addanci, ‘yan bindiga, talauci da gazawar shugabanci, ba wai kawar da wata al’umma ta addini ba.

Ta ƙara da cewa, Musulmi da Kiristoci duk sun sha wahala, amma alƙaluma sun nuna Musulmi ne mafi yawa daga cikin waɗanda rikice-rikice suka shafa a jihohin Borno, Yobe, Zamfara, Katsina, Sakkwato, Kebbi, Neja da wasu sassan Kaduna.

Majalisar ta ce, mutum da ake dangantawa da rubuce-rubuce masu nuna wariya ba zai iya samun cikakken amincewar jama’a wajen jagorantar zaɓe ba. Ta kuma nuna cewa tun bayan bayyanar zarge-zargen, shugaban INEC bai fito ya ƙaryata ko ya nemi afuwa ba.

A ƙarshe, SCSN ta jaddada cewa matsayinta ya ta’allaƙa ne kan halayya da amincin shugabanci, ba addini ba, tare da kira ga al’ummar Kirista da kada su bari a raba su ta hanyar labaran da ke da manufa ta ɓangaranci. Ta kuma sake tabbatar da ƙudurinta na goyon bayan zaman lafiya, adalci da mutunta juna a tsakanin dukkan ‘yan Nijeriya.

By ukarofi