Daga MUKHTAR YAKUBU
A cikin yunƙurin tallafawa masu taɓin hankali da marayun da suke gararamba a tituna, ƙungiyar SAI DA LAFIYA, ƙarƙashin jagorancin Injiniya Ibrahim Sale Gunduwawa, ta gudanar da wani zagaye na tallafi a birnin Kano da kewaye a ranar Asabar da ta gabata.
A yayin wannan aikin, ‘yan ƙungiyar sun bi kan tituna, suna kama masu taɓin hankali, suna yi musu aski da wanka, suna ba su sabbin kaya, sannan suna samar da abincin da za su ci. Haka kuma, marayu sun samu irin wannan kulawa daidai da buƙatunsu.
Shugaban ƙungiyar, Injiniya Ibrahim Sale Gunduwawa, ya bayyana wa wakilinmu cewa:
“Aikinmu shi ne, duk inda muka samu mara lafiya, za mu yi masa aski da wanka, mu canja masa kaya, sannan mu saka a kafafen sada zumunta domin ‘yan uwansu su san inda muka same shi. Idan kuma an samu wanda zai ɗauki nauyin magani, za mu kai su asibiti su biya kuɗin magani.”
A kan tambayar tsawon lokacin da suka shafe suna gudanar da aikin da irin nasarorin da suka samu, ya ce: “A yanzu mun kai kusan shekara guda muna gudanar da wannan aiki, kuma mun taimaka wa mutane da dama. Muna ɗauke da hotunan su da bayanan su; wasu sun samu lafiya. Alhamdulillah, muna samun ci gaba sosai. Muna ganin farin cikin mutane lokacin da muka fito yana ƙara mana ƙarfafawa. Haka kuma, wani mai son alheri ya ɗauki nauyin mutane shida ya biya musu magani.”
Daga ƙarshe, Injiniya Ibrahim ya yi kira ga gwamnati da jama’a da su shiga wannan aikin don tallafawa, yana mai cewa, “Duk abin da muke yi yanzu ana yin sa ne da kuɗin mu, saboda haka muna neman gudunmawar gwamnati da jama’a. Muna buƙatar abin hawa don gudanar da aikin cikin sauƙi; a yanzu muna amfani da babura masu kafa uku kawai. Da gudunmawar jama’a, za mu iya yin aikin cikin sauƙi kuma samun nasarar da ake buƙata.”
