
Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Kebbi
Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabuwar sakatariyar gwamnatin Jihar Kebbi ta zamani a Birnin Kebbi, wadda aka yi wa laƙabi da sunansa.
Tsohon Gwamnan jihar, Sa’idu Ɗakingari ne ya fara gininta, inda gwamnati mai ci a yanzu ta Kwamred Nasir Idris ta kammala tare da ingantata da ginin zamani.
A sa’ilinda yake yanke kyallen buɗe sakatariyar, Shugaba Tinubu, ya yi yaba wa gwamnan bisa yadda ya bai wa kyautatawa da jin daɗin ma’aikata fifiko, da kuma kare ‘yancinsu da haƙƙoƙinsu.
“Ba abin mamaki bane yadda kake kulawa da kuma dora fifiko akan jin dadin ma’aikata, sannan kuma ka nuna shugabanci na kwarai wurin inganta rayuwar al’ummarka”,
“Abokina, kuma dan’uwana na gaske, ina jinjina maka da kuma tayaka murna”,
“Da Allah Maɗaukaki da kuma san-barka na jama’a, abinda kakeyi na raya jihar Kebbi, na amince dashi, kuma ina yaba maka”, cewar Tinubu.
Shi dai Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamred, Dakta, Nasir Idris, Kauran Gwandu, Gwarzon Daular Uthmaniyya, ya rufa ma Shugaban Kasa Tinubu baya, zuwa wurin bude sabuwar sakatariyar, a inda kuma ya kaddamarda wasu ayyukan ci-gaban al’umma masu muhimmanci da gwamnar ya aiwatar, ta hanyar bidiyo, (watau, virtually).
Ayyukan sune mayar da tagwayen hanyar Sarki Haruna da ke Birnin Kebbi zuwa hanya mai hannu-uku ko wani bangare, watau 3-lane, da kuma sabuwar Kauran Gwandu Kwalejin horasda masu koyon jinya da ungwazoma dake Ambursa.
Sauran sune, sabuwar Tashar Mota ta Zamani dake babban birnin jihar, Birnin Kebbi, da kuma maida hanyar bayan-gari dake garin Argungu zuwa tagwayen hanya.
Daga bisani ya shiga jirgin helikopta tareda Gwamna Nasir Idris zuwa bukin kamun kifi na 2026 a Argungu.
“Bayan kammala bukin suka dawo Birnin Kebbi, a inda ya shiga Jirgin Shugaban Kasa, (Presidential Jet) ya koma Abuja daga Filin Jirgin Sama na Sir Ahmadu Bello dake Birnin Kebbi.
Akwai gwamnonin jihohin Kebbi da Sokoto da Gombe da Jigawa da Imo da Zamfara da kuma Kaduna, da suka halarci bukin kamun kifin na Argungu tare da Tinubu.



