Daga AISHA ASAS
“Aure duniya ce guda mai zaman kanta”
(Ci gaba daga makon jiya)
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Gimbiya, sannunku da jimirin bibiyarmu. Ga waɗanda suka samu damar kasancewa da mu a satin da ya gabata, mun ɗauko tattaunawa kan ɗaya daga cikin sanannun ababe marar farin jini a Kasar Hausa, wato zawarci.
Kamar yadda muka tattauna da dattiijiwa Yabi Muhammadu, wannan mako ma za mu waiwayi wasu matan a inda muke buƙatar ƙarin bayani, amma kafin nan, zan so mu karkata akalar rubutunmu kan halin da mata ke shiga yayin da suka baro gidan aurensu.
Yakan yi wuya a Kasar Hausa a samu waɗanda ke damuwa da tambayar halin da macen da aka saka take ciki bayan ta dawo gida. Idan na ce halin da take ciki, ba ina nufin iya abinda za ta yi buƙatu ba, har halin da take ciki na daga sauyin rayuwa da ta samu baki ɗaya.
Sau da yawa mata kan guje wa mutuwar aure ne saboda tsoron barin duniyar da suka yi sabo da ita zuwa wadda ba su saba ba. Rayuwar mace baki ɗaya ce ke canzawa yayin da ta bar gidan miji zuwa wani gidan koda kuwa na iyayenta ne.
Kamar yadda wata baiwar Allah da muka haɗu da ita abgidan gaisu ta ke faɗa, matar mai suna Halima, wadda ba ta fi wata uku da rabuwa da mijinta ba, ta bayyana irin yadda duniya ke tsayawa cak ga mace yayin da aka sake ta, inda ta ce, koda a matsanancin hali mace take a gidan miji, tana addu’a Allah ya raba ta da gidan auren, to fa sai ta girgiza idan aka ce sakin nan an yi shi.
“Ai bari ki ji in gaya maki, shi aure da ki ke gani duniya ce guda mai zaman kanta, ranar da duk ya mutu ko dole ya girgiza mace. Ke gan ni nan ko Aisha, wallahi da zan ba ki labarin baƙar azabar da na sha wurin mijina, da sai ke yi mani hawaye, ta kai ko ruwan ga na sha da aka samu a bohol wuyar samu yake min, don bai sa a kawo min, bai bari na tai na ɗibo, kuma ba ya bari ko almajiri ya shigo gidanshi.
Ya hana ni sana’a ta komai, kuma shi ba tsare mana cin mu ya yi ba. Idan kin tambaye shi kuɗin abinci to ranar sai ke yi kuka, wai ai ya sani har sai an roƙe shi. Wata rana sai a kwana a yini ban ga ko ruwan da za mu sha ba bare abinci, kuma ga rashin fita bare ka je ka nemi naka. Kitso da na ɗan fara a ɓoye in ya tafi kasuwa, ranar nan da ya dawo da wuri, matar da nake wa kitso ba ki ga abinda ya yi mata ba, sai da mijinta ya kai ƙaran shi ga ‘yan sanda.
Amma randa anka ce maki ya kawo takarda saki ga kawuna, da an ka faɗa min, kamar in faɗi, zuciyata ta buga da ƙarfi. Saboda shi aure da ki ka gani rayuwa ce ga mai shi.”
Ita kuwa ɗaya daga cikin matan da ake zaune a wurin mai suna Amina ta bayyana yadda take mamakin yadda mata ke ƙyamatar rabuwar aure, ko in ce zawarci, inda ta danganta ƙyamatar da ake yi masa da zama silan matsaloli da dama da ke samun mata.
A cewar Amina, rashin rabuwar aure a lokacin da auren ya ƙiya ne babbar matsala da ta fi zawarcin.
“Ina mamakin yadda mata ke tsanar mutuwar aure da kalmar bazawara, to meye ranar auren da zai yi sanadin kamuwa da cuta gare ki ko ki aikata ɓarna. Yanzu ke ga ko kashe mazaje da mata ke yi, in ki ka bincika akwai rashin rabuwa lokacin da auren ya kasa.
Miji na gallaza miki, iyaye na cewa ki yi haƙuri. Wani lokacin ko sauraren ki ba su yi, saidai a ce maki kowa ki ka gani a gidan aure haƙuri yake yi. Shi ko miji an ba shi lasisin yin duk yadda ya ga dama, ke ga babu ta inda zai sarara maki, ba a ma lurar da shi bare ya san laifi ya yi. Ga macen da mijinta ke bugunta, ya hana ta abinci, ya hana ta fita, ya mata baƙar magana, ya zage ta ko ya zagi uwayenta, kuma ita babu inda za ta je a yi mata magani, ko ma a bata dama ta faɗi damuwarta don ta ji sanyi. To irin ta don Allah idan zuciya ta ɗebe ta ta rabka mashi wani makami, aka yi daidai da ajalim sai a ce ‘yar isa ce ko a kira ta marar imani ko. Bayan duk haɗuwa aka yi aka yi wannan kisan. Tun ko daga iyayenta da na shi da ake kai ƙaran shi ba su yi masa magana, har zuwa ga al’umma da suka shimfiɗa aƙidar duk runtsi gara mace ta tsaya gidan miji.”
Da muka tambaye ta ko akwai wata mafita ko hanyar da take ganin za a iya bi don kauce wa matsalolin da ta ambata, Amina cewa ta yi, “E, sosai ma akwai, yadda ki ka ji na faɗi wasu matan da yawa al’adar nan ta ƙyamar zawarci ke sa iyaye su kau da ido kan matsalolin da ‘ya’yansu mata ke ci, don haka su ya kamata su fara gyarawa. Babu laifi don ku iyaye kun tsayawa ‘ya’yanku mata a gidan mijinsu, kun nunawa mijin da ke cin zarafin su su ma fa ‘ya’ya ne masu gata, kuma ba ku ba su su ba don su gallaza masu ba. Ku tsaya masu inda suke buƙatar a tsaya masu, ku saurare su idan sun zo faɗa maku damuwar su, bayan kun saurare su sai ku ba su haƙuri. Idan na ɗaukar mataki ne ku ɗaukar masu mataki.
Yanzu misali, a ce miji ya yi wa ɗiyarka ɗan banzan duka, ta zo gida ta faɗa maku, kuma sai ku nuna masa idan shi ɗan zamani ne, kuma fa iyayen zamani ne, sai ku tatake su sa a masa duka irin na ƙato da ƙato, kunga nan an kwatar mata ‘yancinta. Gobe ma da zai ƙara, kuma sai ku ƙara. To tabbas ba jimawa zai bari.
Amma kun ce ta yi haƙuri, ta koma ba wani mataki, gobe ma zai ƙara, jibi ma haka har sai ya hallaka maku ɗiya. Idan kuma auren ya kai maƙura wurin lalacewa, ku kanku ku ka tabbatar da auren ya yi esfaya, to kar ku ce duk runtsi ta zauna, ku shiga cikin lamarin ta samu sa’ida, kuma ku tabbatar mata babu laifi a zamanta bazawara.
Ku bata kulawa irin wadda ta dace, sannan ku tambaye ta halin da take ciki, ko me take so ta yi da rayuwarta. Aure take son idan ta samu miji ta yi, ko neman na kanta, ko kuma karatu take so. Sannan ku kaucewa zargin su. Don gaskiya babbar matsalar da zawarawa ke samu ita ce rashin yarda da su. Shi kenan sai a ta ganin kamar duk inda ta shiga iskanci ta je yi. Wai don ta saba da namiji. To mata nawa ne ke iya riƙe kansu. Akwai mata da yawa idan sun jima da miji sai ya jingine su, ko ran kwanansu ba abinda ka shiga tsakaninsu. Sai su yi watanni ba su ji namiji ba, amma haka za su riƙe kansu ba su iskanci, to ina ga sun san abin nan ba mai samuwa ba ne, kuma ba namijin da ke kwana da su ɗaki guda bare su ji kwaɗayin abin.
Ita fa mace idan iskanci ta sa gaba wallahi ba ruwanta da aure ko rashin sa. Ke da auren ma ya fi sauƙi, don ko tsautsayi ya gitta kin yi ciki, ke san wanda za ki maƙalama shi. Amma kina gidanku, ina za ki ki kwana, sannan ko kina yi ba dai don kin mora ba, saboda ko sa idon na hana ki jin daɗin abinda ki ke yi. Sau da yawa mata na lalacewa ne idan suna gida don neman na buƙatunsu. Wanda ita ce matsala da nika so in faɗa maki a matsayin babban ƙalubalen da mata zawarawa ke fuskanta.
Ke gane ni nan, lokacin da aurena ya mutu, wanda ba wani wahalar da ni ya yi ba sosai, mamarshi ce dai tun farko ba ta so auren ba, shi kuma ya nace, mu kuma gidanmu ba mu sani ba sai bayan an yi auren. To ƙiyayyar da take yi min ce ta sa kullum cikin faɗa muke da shi, kin san tsakanin uwa da ɗa sai Allah, to har dai aka kawo ya sake ni a wani faɗa.
Da na dawo gida, bayan an gama jimame da sauransu. Ana dai sawo min tuwo daga gidan yayanmu da ke tsallake kullum bayan azahar idan an gama. Amma kinga karin safe, ke ga sabulun wanka da na wanki, bare mai da ɗan abin kwalliya da turare, ko kaɗa irin tamu ta mata, ban taɓa sanin ranar da wani ɗan uwana cikin ‘yan uwa takwas da nake da su maza ya ɗauko ɗaya daga ciki ya nufato ni ba. Ko ya ba ni kuɗi ya ce na siye ba.
Kuma babu wanda ya taɓa taro na ya ce wance wacce sana’a ki ke son ki yi na tallafa miki ki dogara da kanki. Kuma babu wanda ya ma taɓa tambaya ta ya nake buƙatuna tunda ban da uwa ta rasu.
To irin wannan Aisha don Allah idan ba tsoron Allah ba me zai hana macen da ba ta san yadda ake nema ba, ko ba ta da abin da za ta yi nema faɗawa halin iskanci. Ke san dai yadda mazan yanzu suke kamar bunsuru, dama kawai suke nema, bare sun ga mabuƙaciya ki ke. Sai ke yi abinda bai dace ba a dawo a shirya maki zama na musamman a sanar da ke ba ki kyauta ba.
Ba wai na ce duk macen da ke iskanci dalilin kenan ba, asali ma ko wadda take cikin irin halin da na faɗa ba hujja ba ce da za ta sa ta tayi isakanci ba, don ba a kanta farau ba, yadda wata ta yi haƙuri, ita ma haka ya kamata ta yi.”
