
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin ne jiga-jigan APC suka amshi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zuwa cikin jam’iyyar a hukumance a Fili wasa na Sani Abacha da ke jihar.
Wannan taro ya tara dubunnan magoya baya, jagororin jam’iyyar, ‘yan majalisun tarayya da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa daga sassan Nijeriya, lamarin da ke nuna muhimmancin sauya sheƙar gwamnan zuwa APC.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana Kano a matsayin jihar da ta ƙware wajen iya amfani da dabarun siyasa da za ta taimaka wa bunƙasar harkokin jam’iyyar.
Ya bayyana cewa, babu wani ɗan siyasa da zai cire rawar da Kano ke takawa wajen ciyar da dimukraɗiyyar Nijeriya gaba, yana mai taya Abba murna bisa abin da ya kira da mataki na hangen nesa bisa jajircewa.
Haka kuma Mataimakin Shugaban Ƙasar ya isa da saƙon jajenta wa waɗanda iftila’in gobarar kasuwar Singa ta same su, inda ya sanar da amincewar Gwamnatin Tarayya ta bayar da tallafin Naira biliyan 5 a gare su domin rage musu raɗaɗi.
