Daga ALI ABUBAKAR SADIK
’Yan Najeriya sun wayi gari katsam da sanarwar Babban Daraktan gudanarwa na hukumar aikin Alhazai ta kasa, Sheikh Sale Pakistan cewa yayi Murabus na kashin kansa, a wata takarda da ya aikewa shugaba Bola Tinubu. Sanarwar ta katsam ce, amma duk wanda ya ke bibiyar dambarwar da ke faruwa a hukumar ya san cewa sai an zo wannan wurin ko ba daɗe, ko ba jima.
Idan ma banda kasa irin tamu, ai babu ta yadda za’a yi a baiwa Sheikh Sale Pakistan rike amanar wannan hukumar Mai matukar tasiri a kasar. Dalili kuwa shine idan ba mu manta ba, a lokacin badakalar Gandollar bayan bidiyo ya karade ko’ina, Sheikh Sale Pakistan, a matsayin shugaban Izala na jihar Kano, ya tattaro malamai inda su ka kai wata ziyarar goyon baya ga Ganduje a fadar gwamnatin Kano, inda a wajen Taron, a Radio, ya bayyana cewa sun san cewa sharri ake neman Ganduje da shi, kuma kamar yadda Allah ya wanke Nana Aisha daga zargin Zina, haka su ke sa ran Allah zai wanke Ganduje daga zargin cusa Dala.
Duk malamin da zai yi wannan, kai ko ba malami wanda ya san kalallahu kala rasulu ba, to ai bai kamata a bashi wata Amana ta dukiyar jama’a ba. To amma dai idan ma wadancan kalamai nasa ba su sa aka gane haɗarin ba, yanzu yadda kafatanin membobin hukumar da ke wakiltar shiyyoyi shida na kasar nan sun tabbatar mana. Domin a cikin wani koke da dukkan membobin hukumar su ka saka hannu wadanda su ka hada da Professor Muhammad Umaru Ndagi (North-Central), Alhaji Abba K. Jato (North-East), Shaykh Muhammad Bn Uthman (North-West), Hajiya Aishat Obi (South-East), Hajiya Zainab Musa (South-South), Dr Tajudeen Abefe Oladejo (South-West), da kuma wakilai biyu, wato Professor Adedimeji Mahfouz Adebola daga NSCIA da kuma Professor Musa Inuwa Fodio na JNI, sun aikewa ofishin Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, suna zargin Malamin da badakaloli daban daban da neman a tsige shi daga mukamin.
Haka kuma hatta ma’aikata na hukumar, su kansu sun rubutawa shugaban wata takardar koke kan rashin kula da walwalarsu da kuma nuna son kai ko wariya tsakanin ma’aikatan. Kungiyar kamfanoni masu shirya zirga-zirgar aikin hajji da umara (AHOUN), su ma sun yi nasu korafin akan shugaban da irin nasu matsaloli kama daga wariya da kuma rashin dawo musu da wasu kudade nasu a baya.
Don haka daga dukkan alamu dai ka san abinda ya koro bera ya fada wuta, to ya fi wutar zafi ne. Wataƙila wannan dalili ne ya sa Sheikh Pakistan ya gwammace rufa wa kansa asiri ya sauka daga wannan kujera, ’yan watanni da a fara aikin hajji na wannan shekara.
A taƙaice, wajibi ne malamai idan su na son su rike matsayinsu na “Magada annabawa” lallai ne idan ba za su iya tsayawa a hurumin malanta kawai ba, idan har za su shiga siyasa da gudanar da al’amuran jama’a to lallai ne wajibi su kasance sun nuna halayya mai tsafta musamman a kan dukiyar jama’a. Sannan dole su yi koyi da magabata wajen karfin halin su kalli masu mulki a cikin idonsu su gaya musu gaskiya, sannan su kuma iya kwabarsu idan sun yi ba daidai ba, maimakon amfani da addini domin basu kariya su ci gaba da aikata ba daidai ba.
Arewa na gab da rushewa, saboda manyanmu (’yan siyasa, malamai da ’yan boko) sun saka samun abun duniya kaɗai a gabansu, kuma idan sun samu, babu ruwansu da kowa sai matansu da yayansu. A yadda mu ke ta hayayyafa ba tsari ba kula ba tanadi na ilimintarwa da samar da aikin yi, wallahi wagegen ramin da muke dosa sai ya hadiye mu. Wannan sakaci na gaza rarraba arziki ta hanyar zuba jari a noma da Ilimi mun ga inda ya fara kaimu a yanzu, wato Boko Haram, ta’addanci da satar mutane. To nan gaba kadan Allah kadai ya san mai zai bullo idan ba mu fara rarraba arziki ta hanyar samarwa wadannan matasa ayyuka ba.
Ali manazarci ne mazaunin Kano
