
An bayyana matan Ƙaramar Hukumar Bichi a matsayin masu kishi da ƙwazo bisa haɗin-kai da suke ba da wa wajen koyan sana’o’in dogaro da kai.
Daraktan Mulki na yankin, Alhaji Abba Muhammad Ɗiso ne ya bayyana haka, a yayin da ƙaramar hukumar ta karɓi baƙoncin tawagar mai bai wa Gwamna Shawara a kan al’amuran Aikin Gayya da Sa-Kai na jihar Kano, Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya.
Daraktan Mulki, Alhaji Abba Muhammad Ɗiso, ya kuma jaddada matan yankin burinsu shi ne, inganta zamantakewar aure a tsakanin iyalai domin kyautata tarbiyyar yara, kasancewarsu manyan gobe da za a iya samun shugabanni a cikinsu, daga bisani kuma ya jinjina wa Gwabnatin Jihar Kano bisa ƙoƙarinta na taimaka wa al’amuran jama’a makamantan haka.
“An yi gwamnoni da dama a Kano, amma kowa ya san irin yadda ake ayyuka a Jihar Kano a yanzu dole akwai bambanci gaskiya. Don haka muna godiya da waɗannan ɗimbun ayyuka na alheri tare da irin yadda Gwamna yake naɗa rinku waɗanda kuka san aikinku.” Alhaji Abba Muhammad Ɗiso
Shi kuwa mai bai wa Gwmna Shawara a kan Ayyukan Gayya da Sa-kai,. Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya, ya bayyana maƙasudin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke waiwaye tare da bijiro da ingantattun ayyukan inganta rayuwar al’uma kacokan a fadin jihar nan.
“Game da maganar ayyuka na cigaba, gwamnatin Kano burinta shi ne duk wanda yake da burin ya taimaka wa kansa da kuma sauran al’uma, shi ma gwamnati za ta taimaka masa, wannan shi ne dalilin da ya sa muka zo mu tattauna mu ga irin yadda za mu tattara bayanan buƙatunku da za mu tura wa mai girma Gwamna, shi kuma ya ga irin gudunmawar da zai bai wa Ƙungiyoyin Aikin Gayya na taimakon kai-da-kai domin haɓaka rayuwarmu da tattalin arzikinmu.” Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya
A jawabin Shugaban Ƙungiyar Aikin Gayya, Malam Garba Tsoho tare da Ma’ajin ƙungiyar ta Ƙaramar Hukumar Bichi, Malam Yusuf Tambai Ɗansiri, sun gode da wannan gagarumar ziyara ta farfaɗo da harkokin Ayyukan Gayya a kafatanin Jihar Kano, inda suka bayyana ƙalubalen da suke fuskanta duba da manufofin ziyarar.
“Akwai alawus da ake badawa na ko’odinetin kwamiti a da can, amma shekara da shekaru da suka wuce aka daina bayarwa, hakan kuma yana ɗaya daga cikin abubuwan da suka haifar da koma-bayan cigaban ayyukan gayya, sannan akwai buƙatar kayan aiki da ake badawa irinsu shebura, diga da sauransu, kuma a halin yabzu gaskiya ba mu da su.” Yusuf Tambai Ɗansiri
“Ya kamata don Allah don Annabi a duba a dawo da irin waɗannan abubuwan saboda su ne za su farfaɗo da ayyukan gayya, kuma a nuna wa ƙananan hukumomi mahimmancinsu domin su yi ƙoƙari su sayi kayayyakin aikin gayyan nan, in Allah ya yadda muddin aka samu hakan za a samu cigaba. Mu kuma duk sadda aka neme mu, ko dare ko rana a shirye muke mu shiga kashi ko kwata mu gyara dukkan wajen da ake son tsaftacewa.” Malam Garba Tsoho
A ɓangaren shagabannin ƙungiyoyin bunƙasa al’amuran matan yankin ta fuskar sana’a da suka haɗa da; Malama Rakiya Abdullahi Bichi, sun buƙaci gwamnatin jiha ta tallafa musu da abubuwan koya wa mata sana’o’i da suka kunshi; kekunan ɗinki da injinan saƙa da kiwon kaji da kuma wajen noman rani da damina a ɓangaren kwaminiti.
