Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da tallafa wa mata 500 da suka sami horo kan sana’o’i

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da shirin tallafa wa mata 500 da suka kammala horaswa a sana’o’i, wanda gidauniyar Auwal Lawal Daura (ALD) Foundation ta shirya.

An gudanar da taron a garin Daura, tare da tallafin kuɗi domin su fara ko faɗaɗa harkokinsu. Kowace mahalarta ta samu jari na farko domin ƙarfafa sana’arta da fara kasuwanci iri-iri.

Daga cikin sana’o’in da aka tallafa akwai ɗinki, ƙera takalma, yin sabulu, turare, man girki, da sauran sana’o’in da suka shafi ƙamshi.

A jawabin sa, Gwamna Raɗɗa ya yaba wa gidauniyar ALD bisa jajircewarta wajen ƙarfafa mata da matasa.

Ya jaddada muhimmancin irin waɗannan shirye-shirye wajen bunƙasa cigaban al’umma, ‘yancin tattalin arziki, da kuma kyakkyawar zamantakewar ‘yan ƙasa.

“Wannan shiri ba wai koyon sana’a kaɗai ba ne, har ma da ƙarfafa iyalai da ɗaga martabar al’umma,” in ji shi.

Gwamna Raɗɗa ya kuma yi alƙawarin ƙarin tallafin kuɗi domin tabbatar da cewa matan sun aiwatar da ƙwarewar da suka samu, yana mai jaddada cewa al’ummar Katsina su ne ginshiƙan waɗannan shirye-shiryen tallafin.

Tun da farko, Shugaban Gidauniyar ALD, Alhaji Auwal Lawal Daura, ya nuna godiya ga Gwamna Raɗɗa bisa goyon bayan da yake bayarwa ba tare da gajiyawa ba.

Ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen ɗaga darajar mata da matasa, yana mai bayyana cewa gidauniyar na mayar da hankali kan haɓaka ƙwarewa, kasuwanci, da ci gaban al’umma.
“Idan aka ƙarfafa mata, ba iyalansu kaɗai suke tallafawa ba, har ma suna ba da gudummawa mai kyau ga al’umma baki ɗaya,” in ji Daura.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati ciki har da Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, Babban Sakataren Gwamna, da sauran manyan jami’ai, tare da ɗaruruwan waɗanda suka ci gajiyar shirin.

Gwamnan daga baya ya bada gudummawar Naira miliyan 2.5 ga matan.

By ukarofi