El-Rufa’i na komarmu bayan DSS ta ɗauke shi daga ofishin EFCC, inji ICPC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Yaƙi da Laifukan Rashawa da Makamantansu (ICPC) ta tabbatar da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i na ƙarƙashin ikonta bisa binciken da ake yi akansa na wasu tuhume-tuhume da aka gabatar masa.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’arta, Mista J. Okor Odey ya fitar, ICPC ta ce El-Rufa’i yana hannunta har zuwa lokacin tashi a aiki na ranar 18 ga Fabrairu, 2026.

Saidai hukumar ba ta yi ƙarin haske akan al’amarin binciken ba, amma ta tabbatar wa al’umma cewa za a bi hanyoyin da doka ta tanada wajen bayyana dukkan abin da ya kamata a sani akan al’amarin.

Hakan na zuwa ne yayin da El-Rufa’i ke tsaka da fuskantar bincike akan badaƙalar wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai biliyan N432 a lokacin da yake riƙe da muƙamin gwamnan Jihar Kaduna.

A farkon makon nan ne El-Rufa’i ya kai kansa ofishin Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) bayan gayyatar sa akan zargin hannu a rashawa tsakanin 2015 da 2023, wato sadda yake gwamna.

Tun a ranar Litinin EFCCn ta tsare shi har zuwa lokacin da aka bayar da belinsa da misalin ƙarfe 8 na dare a Laraba.

Jim-kaɗan bayan haka ne aka yi zargin jami’an Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) sun ɗauke shi daga babban ofishin EFCCn a Abuja. Daga bisani suka garzaya da shi hedikwatar DSS a Asokoro da ke birnin tarayyar.

By Babaji