
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla masu aikin haƙar ma’adanai 30 ne suka rasu yayin da wasu guda 20 ke kwance a asibiti bayan shaƙar wata iska mai guba da ake zargin ‘carbon monoxide’ ce a wani wurin haƙar ma’adanai da ke Ƙaramar Hukumar Wase a Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata wurin a wani ƙauye da ake kira Zuruk, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa manema labarai.
Wani daga cikin mutanen ƙauyen ya ce masu haƙar ma’adanan na cikin rami a lokacin da hayaƙin gubar ya turnuƙe su, inda da dama daga cikinsu suka gagara fitowa daga ciki.
Tuni aka yi jana’izar mamatan, waɗanda shekarunsu suka kama daga 20 zuwa 40, jim-kaɗan bayan faruwar iftila’in.
Saidai duk da haka, an yi nasarar ceto mutane 20 waɗanda aka garzaya da su asibiti, inda a yanzu ba a san halin da suke ciki ba.
Bayanai sun ce jami’an ƙaramar hukumar na shirin zuwa yankin domin tantance abin da ke faruwa, duk da cewa ayyukan kai ɗauki na fuskantar cikas saboda matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, ba a samu wani bayani a daga gwamnatin jihar ko hukumomin tsaro ba.
