DSS ta yi ram da El-Rufa’i bayan barin hannun EFCC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yammacin Laraba ne jami’an Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, suka cafke Malam Nasir El-Rufa’i jim-kaɗan bayan ya bar hannun Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC).

Bayan kama shi ne, jami’an suka tsare shi, kamar yadda wata majiya mai ƙarfi ta shaida wa Blueprint.ng.

Tsohon Gwamnan Jihar Kadunan na fuskantar sabon ƙalubalen ne bayan shafe kwana biyu a garƙame a hannun EFCC kamar yadda rahotanni suka bayyana.

DSS ta kama shi ne bisa zargin yin kutse a wayar Mai bai wa Shugaban kasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu.

El-Rufa’i ya shafe kwanaki biyun ne a hannun jami’an hukumar akan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati a lokacin da yake riƙe da madafan iko a matsayin gwamnan Kaduna.

Haka ma, Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka da Rashawa (ICPC), ta gayyaci shi bisa tuhumar da Majalisar Dokokin Kaduna da yi akansa na badaƙalar kuɗaɗen da adadinsu ya kai jimillar biliyan N432.

By Babaji