Tinubu ya yi kira ga malamai da sarakuna su sa hannu wajen yaƙi da cutattuka a Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci sarakuna da malaman addini kan su sa hannu a yaƙin da ake yi wajen gujewa kamuwa da cututtuka, yana mai cewa kula da lafiyar ‘yan Nijeriya nauyi ne a kan kowa.

Shugaba Tinubu ya yi wannan kira ne a ranar Talata a yayin da yake magana a taron malamai da sarakuna da kiwon lafiya da aka yi a gidan gwamnati a Abuja.

“Yaƙi da cututtuka nauyi ne a kan kowa, kuma a matsayina na shugaban ƙasa, ga ni a gabanku cikin mutuntawa, ina tabbatar muku cewa wannan nauyi ne a kanku sarakuna.”

Shugaban ƙasa ya bayyana taron da wanda ke cike da hikima da ƙarfin guiwa.

Shugaba Tinubu ya gode wa shugabannin kan irin yadda suka himmatu wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya da a duk inda suke.

“Wannan girmamawa ce yadda na samu damar sauraronku da irin yadda kuka himmatu wajen inganta lafiyar ‘yan Nijeriya,” in ji Tinubu.

Ya ce in ba don shugabannin ba da sauye-sauyen da gwamnatinsa ke kawowa da ba za su kai ga al’umma ba saboda su ne ke tsakanin gwamnati da al’umma.

“Ba wani sauyin na ɓangaren lafiya da zai yiwu ba tare da ku ba. Muryoyinku da aka aminta da su, su ne gadar da ke haɗa gwamnati da al’umma.”

Shugaban ƙasa ya tuna da yadda gwamnatinsa ta faɗaɗa shirin bunƙasa lafiya na “Uniɓersal Health Coɓerage Compact” ta yadda zai ƙunshi har da malamai da sarakuwa da al’umma da ɓangarori masu zaman kansu.

Shugaba Tinubu, ya ce, mutuwar mata masu juna biyu da lafiyar jarirai da allurar rigakafi da magance ɓarkewar cutattuka da samar da abinci mai gina jiki da wadataccen abinci na ci gaba da zama muhimmin abu na tallafa wa na ƙasa-ƙasa.

“Al’umma ku suke fara sauraro kafin su saurari gwamnati,” ya faɗa.

Shugaban ƙasa ya buƙaci sarakunan da su sa ido kan yadda asibitoci a matakin farko ke aiki a garuruwa da kuma tura rahoto a kai domin a ɗauki mataki.

“Ku duba asibitocin da ke kusa da ku, ku tura a duba muku asibitoci, idan ba sa aiki ku sanar mana ko ku rubuta wa ƙananan hukumomi ko jiha ko gwamnatin tarayya. Za mu ɗauki mataki,” ya bayyana.

Ya kuma yi magana kan shirin bunƙasa lafiya ta ƙasa wanda ya ƙunshi tura likitoci zuwa ƙananan hukumomi 774 domin inganta kiwon lafiya da rage mutuwar mata da ƙananan yara.

“A shekarar 2025, mun ɓullo da shirin “National Health Fellowship” inda muka zaɓi gwarazan likitoci matasa tare da tura su ƙananan hukumomi 774 da suke ƙasar nan,” ya fada.

Shugaba Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta yin komai a buɗe da shigo da kowa da kowa inda ta buƙaci samun haɗin kan al’umma domin samar da ingantaccen tsarin lafiya da samun haɗin kan ‘yan Nijeriya.

By ukarofi