Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe dukkan yankunan da ke ƙarƙashin lasisin haƙar ma’adinai mai lamba ML 11810 a ƙaramar Hukumar Wase, jihar Filato, bayan rasuwar mutane 37 da ake zargin sun mutu sakamakon shaƙar iskar guba a wani rami na haƙar ma’adanai.
Ma’aikatar Ma’adanai ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce kamfanin Solid Unit Nigeria Limited, mallakar Abdullahi Dan-China a Zurak, shi ne ke da lasisin wurin.
Ministan ma’adinai, Dele Alake, ya yi ta’aziyya ga Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, bisa wannan mummunan lamari da ya yi sanadiyyar mutuwar mazauna yankin da ke ƙoƙarin neman abin dogaro da kai.
Ministan ya kuma tura tawagar bincike ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren ma’aikatar, Yusuf Yabo, domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma ba da shawarar hukuncin da ya dace.
Tawagar ta ƙunshi kwararru a ɓangarorin haƙar ma’adanai, kula da muhalli da kuma haɗin gwiwar masu haƙar ma’adinai na gargajiya.
A cewar sanarwar da mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Segun Tomori, ya sanyawa hannu, rahotannin farko sun nuna cewa kamfanin ya bai wa al’umma damar haƙo ma’adinai a cikin ramin bayan matsin lamba da matasa suka yi na a ba su dama su samu sana’a.
Bincike ya nuna cewa wurin tsohon ma’adinan gubar lead ne da aka bari, kuma yana ɗauke da ma’adinai masu saurin fitar da iskar sulphuric oɗide mai guba. Ba tare da sanin hatsarin iskar ba, mazauna yankin sun shiga haƙo ma’adinan, suna shaƙar iskar da ta yi sanadiyyar mutuwarsu nan take.
Lasisi mai lamba ML 11810 na tsakanin tsayin 10.34.45 zuwa 10.35.50 da kuma faɗin 9.13.45 zuwa 9.14.40. Ministan ya yi alƙawarin cewa za a fitar da ƙarin bayani yayin da bincike ke gudana.
Shugaban matasan Wase, Shafi Sambo, ya ce ya samu kiran gaggawa da asuba kan faruwar lamarin. Ya bayyana cewa ma’adanan sun zurfafa haƙar ramin, inda suka fuskanci iskar guba da ta kashe 37 daga cikinsu a take.
Ya ƙara da cewa, an ceto wasu da dama da ransu, inda aka garzaya da su asibitoci domin samun kulawar gaggawa, sai dai har yanzu ba a tantance adadin waɗanda suka tsira ba. Sambo ya kuma bayyana cewa matasan na haƙar zinc ne a madadin wani kamfani da ake zargin mallakar ‘yan ƙasar Chana ne, duk da cewa ba a tabbatar da haƙiƙanin ma’adinan da ake haƙowa ba.
Lamarin ya sake jaddada buƙatar tsaurara dokoki da sa-ido a harkar haƙar ma’adinai, musamman a yankunan karkara, domin kare rayukan al’umma da muhalli daga irin waɗannan munanan haɗurra.
