Kisan DPO a Katsina ya sa kokwanton ɗorewar sulhu da ’yan bindiga

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina 

Kashe DPO ɗin ’yan sanda a yayin wani farmaki da ‘yan bindiga suka kai a Jihar Katsina ya sa kokwanto kan tabbacin yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi da ‘yan bindiga duk da irin nasarorin da jami’an tsaro ke cewa sun samu.

Mahukunta sun tabbatar da cewa Muhammad Kabir, wanda babban sufurtandan ’yan sanda ne kuma DPO na ƙaramar hukumar Rimi,an harbe shi ne a ranar Alhamis data gabata a yayin da yake jagorantar tawagar ‘yan sanda don daƙile wani hari da ‘yan bindigar suka kai inda suka sace shanu masu tarin yawa, ‘yan sandan sun samu nasarar kashe wasu mutane 3 da ake zargin ɓarayin shanu ne a ƙauyen Magaji da ke ƙaramar hukumar Rimi.

Wannan arangama na zuwa ne bayan bayanan sirri da ‘yan sanda suka samu daga kamfanin da ke sa ido kan al’amuran tsaro kafin samun tabbacin mahukunta.

Lamarin ya nuna yanayi mai tada hankali duk da nasarar da jami’an tsaro ke samu a kan ‘yan ta’adda.

Mutuwar Kabir ɗaya daga cikin waɗanda aka rasa a yayin arangamar na zuwa ne lokacin da aka yi yarjejeniyar zaman lafiya da ɓarayin daji da nufin magance matsalar tashe-tashen hankula a yankunan karkara.

Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta bayyana yadda aka kashe mata babban jami’in duk da yarjejeniyar sulhu da wasu al’umma suka yi da ɓarayin, ‘yan sandan sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari da sanyin safiya a garin Magaji inda suka sace shanu tare da kora su cikin daji.

A cewar rundunar ‘yan sandan Katsina, DPO na garin Rimi ya ja zugar jami’an tsaro da haɗin guiwar ‘yan sandan bayan samun kira na neman taimako.

Tawagar Jami’an tsaron ta bi diddigin waɗanda ake nema zuwa garin Magaji inda suka yi musayar wuta da ɓarayin.

Kakakin ‘yan sanda, Abubakar Aliyu, ya ce jami’an tsaro sun ƙwato shanun da aka sace a yayin musayar wutar.

Sai dai DPO Kabir, ya samu gagarumin rauni a wannan musayar wuta inda aka garzaya da shi asibiti kafin daga bisani ya rasa ransa.

Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta tabbatar da cewa mutuwar jami’in ɗan sandar ya zama koma baya a yaƙin da ake da ‘yan ta’adda.

By ukarofi