An naɗa Rabaran Zakwoi a matsayin mai ba kwamitin Tinubu shawara a harkokin addini

Spread the love

DAGA JOHN DOGO WADA, a Keffi

Wani babban malamin addinin Kirista wanda ƙungiyar siyasar nan dake fafutukar tabbatar da sake zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 wato Renewed Hope Independent Support Groups Committee ta naɗa masa muƙamin mai bai wa kwamitin shawara akan harkokin addini, Rabaran Dr. Emmanuel Akawu Zakwoi yace a shirye yake ya sauke sabon nauyin da aka ɗora masa ta hanyar bai wa kwamitin Renewed Hope Independent Support Groups Committee ɗin da kuma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawarwari nagari da za su tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin manyan addinan nan biyu wato Kirista da Musulmi.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai ciki har da wakilin mu jim kaɗan bayan an kaddamar da shi da wasu shugabannin kwamitin reshen jihar Nasarawa a garin Masaka ƙaramar hukumar Karu.

Rev. Dr. Emmanuel Akawu Zakwoi wanda har ila yau shine babban Rabaran na cocin Yoke Breaker Advocacy Ambassador Foundation (YBAAF) dake Masaka ya kuma yi amfani da damar inda ya godewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ƙungiyar dangane da naɗa masa muƙamin inda ya tabbatar masa cewa zai yi aiki tuƙuru don cimma burin kwamitin ɗin da kuma haɗa kan duka addinan biyu a jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya.

Malamin addinin Kiristan wanda aka ƙaddamar da shi a matsayin sabon mai bai wa kwamitin shugaban ƙasa shawarar ya kuma yi amfani da damar inda ya shawarci al’ummar Kirista baki ɗaya su tabbatar sun samu katin zaɓen su kana su fito ƙwansu da kwarkwata suma a dama dasu a duka zaɓukan gamagari na shekarar 2027 dake tafe don a cewar sa lokaci ya wuce da za su zauna su zura ido ana yi banda su.

Tun farko a yayin babban taron ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar Renewed Hope Independent Support Groups Committee, wakilinmu ya kuma ruwaito cewa bayan ƙaddamar da shi babban malamin addinin Kirista din Rev. Dr. Emmanuel Akawu Zakwoi an kuma bashi wani lambar yabo ta musamman tare da miƙa masa satifiket na wannan sabon muƙamin nasa don kama aiki gadan-gadan.

Shi dai sanannen babban malamin addinin Kirista ɗin wato Rev. Dr. Emmanuel Akawu Zakwoi bincike ya gano cewa ya daɗe yana bayar da gagaruman gudumawa musamman a al’amura da suka shafi harkokin addini inda yake aiki tuƙuru ba dare ba rana don tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya tsakanin manyan addinan nan guda biyu a jihar ta Nasarawa da ƙasa baki ɗaya da hakan nema ya jawo hankalin kwamitin da kuma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kansa aka naɗa masa muƙamin.

By ukarofi