
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar shirya jarabawar neman gurbi a makarantun gaba da sakandare (JAMB) ta musanta umartar ɗalibai mata su riƙa cire hijabinsu yayin rajista ko ɗaukar hoton fasfo da za a yi amfani da shi a jarabawar UTME.
JAMB ta bayyana haka ne bayan wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta da ke nuna zargin cewa ana nuna wariya ga wata ɗaliba Musulma a Jami’ar Afe Babalola (ABUAD).
Idan ba a manta ba, a shekarun baya an rika samun koke-koke da suka shafi zargin nuna wariyar addini a wasu cibiyoyin jarrabawar JAMB.
A wata sanarwa da ta wallafa ranar Asabar, JAMB ta bayyana cewa ba ta taɓa fitar da wata doka da ta haramta wa ɗalibai mata sanya hijabi ba.
Ta kuma ce a ƙasashe da dama na duniya, idan ana ɗaukar hoton bayanan halitta (biometric) don fasfo na ƙasa-da-ƙasa ko neman biza, ana buƙatar kunnuwa su fito, kuma abin da ya faru ke nan a ABUAD.
