An kammala zangon farko na ɗaukar fim ɗin ‘Five Winners’  

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

A yanzu haka dai an kammala zangon farko na ɗaukar wani gawurtaccen fim mai dogon zango wanda Kamfanin Jammaje Production ya ɗauki nauyin shiryawa inda aka shafe kusan kwanaki ashirin ana gudanar da aikin.

Fim ɗin mai suna ‘Five Winners’ dai tun kafin fara aikin sai da aka yi masa shiri na musamman ganin yadda aikin fim ɗin zai ɗauki tsawon lokaci da kuma maƙudan kuɗaɗe.

A tsawon kwanakin da aka yi dai ana aikin abubuwa sun faru da dama wanda hakan ya mayar da fim ɗin na daban a cikin ayyukan fim da aka daɗe ba a ga kamar sa ba a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood. 

Domin kuwa fim ɗin ya tara jarumai masu yawan gaske wanda ba ƙaramin kamfani ba ne zai iya hakan a ce an tara jarumai sama da 100 a lokaci guda suna aiki. To shi wannan fim ‘Five Winners’  ya ciri wannan tutar na tara jarumai masu yawa kuma mafi yawancin su sabbin jarumai ne.

A lokacin da muke jin ta bakin babban furodusan fim ɗin ‘Five Winners’ Malam Kabiru Musa Jammaje kan yadda aikin ya gudana. Ya ce, “wannan aikin na ɗauke shi a matsayin wani fim da ya zo da wani sabon salo na koyar da matasa darasin rayuwa musamman ma dai ga masu sha’awar yin karatu da kuma kishin dogaro da kan su.”

Malam Kabiru Musa Jammaje wanda fitaccen Malamin Turanci ne kuma furodusa da ya shirya finafinai masu yawa da harshen Turanci a Kannywood ya ce, aikin ya tafi yadda ya kamata, kuma jarumai sun yi ƙoƙarin bayar da abin da ake so domin suna bin labarin yadda ya dace, wanda su kansu ‘yan Kannywood suke mamakin yadda hakan ta kasance. Domin da yawan jaruman waɗanda suka samu horo ne a makarantar Jammaje Academy ɓangaren koyar da aktin.

Ya ƙara da cewa, “Duk da ban taɓa yin fim mai dogon zango ba sai wannan gaskiya ni kaina abin ya burge ni domin ko a yanzu na samu darasi domin kowanne aiki akwai nasara da kuma ƙalubale.”

Dangane da labarin kuwa Jammaje ya ce ” Labari ne mai kyau wanda mutane idan suka kalla za su samu ilimi a ciki, domin mun zo da wani sabon tsari da babu irin sa a Kannywood, kuma daman ba wai alfahari ba kamfanin Jammaje Production ya yi suna wajen samar da finafinai masu inganci tun a baya. Domin shi wannan gasa ce aka shirya a tsakanin wasu ɗalibai a kan kimiyya da adabim Turanci da Hausa. Don haka wannan fim ɗin idan mun kammala za mu bai wa gidajen talabijin sannan kuma za mu saka shi a YouTube ɗin mu mai suna Kabiri Musa Jammaje wanda hakan zai bai wa kowa damar ya kalla.”

By ukarofi