Yanzu-yanzu: INEC za ta sanar da sabon jaddawalin zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da cewa za ta sake nazari akan kundin dokokin zaɓe na 2026 domin dacewa da doka, bisa la’akari da tsare-tsaren babban zaɓen 2027.

Sakatare kuma mai ba Shugaban INEC shawara akan harkar yaɗa labarai, Mista Adedayo Oketola ya ce hukumar za ta fitar da sabon jaddawalin zaɓen da zarar an kammala nazari akan dokokin.

Duk da cewa mashawarcin bai bayyana takamaiman lokacin da za a fitar ba, ya ce INEC tana aiki tuƙuru wajen ganin ta yi biyayya ga dokokin Nijeriya sau da ƙafa.

Oketlo ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar PUNCH inda ya yake amsa batun buƙatar fitar da wani jaddawalin zaɓen, wanda wasu jam’iyyun siyasa suka gabatar.

Wasu jam’iyyu sun shaida wa jaridar cewa wajibi ne a samar da wani jaddawali bayan sanya hannu a sabuwar dokar zaɓe da Shugaba Bola Tinubu ya yi a makon da ya gabata.

Sun ƙara da cewa, hakan yana da muhimmanci duba da cewa zai ba su damar shirya zaɓukansu na fidda gwani da gudanar da wasu harkokinsu na cikin gida cikin sauƙi yayin tunkarar babban zaɓen.

A makon da ya gabata ne hukumar zaɓen ta ayyana 20 ga Fabrairu da 6 ga Maris, 2027 a matsayin lokutan babban zaɓen.

Lamarin da ya janyo cece-kuce acikin ‘yan Nijeriya musamman al’ummar Musulmi ganin yadda hakan ya yi daidai da lokacin azumin watan Ramadana.

By Babaji