Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa, jihar tana ci gaba da kasancewa babbar matattarar ci gaban tattalin arziki a Nijeriya, inda take bayar da kaso 22 cikin ɗari ga jimillar samun arzikin cikin gida (GDP) na ƙasa bakiɗaya.
Sanwo-Olu ya yi wannan bayani ne yayin zaman Majalisar Kasuwanci a taron Oniru Business and Cultural Day da aka gudanar a daren Asabar a Legas, inda ya ce jihar ta ba da kusan ɗaya cikin biyar na jimillar GDP na ƙasa.
Gwamnan ya ce, wannan ci gaba ya samo asali ne daga zaɓuka na shugabanci da sauye-sauyen da aka aiwatar cikin natsuwa, ta hanyar shirin ci gaban THEMES+, wanda ya ƙarfafa tushe na arziki mai ɗorewa.
Ya kuma yi wa al’umma da ‘yan kasuwa alaawari cewa jihar za ta ci gaba da kasancewa wurin kasuwanci mai jan hankali, tare da mayar da hankali kan ingantaccen ababen more rayuwa, samar da ayyukan yi, ƙarfafa matasa, da tsaro.
Ana wakiltar gwamna a wurin taron ne ta hanyar Mataimakinsa, Dr Obafemi Hamzat, wanda ya jaddada cewa gwamnatin za ta ci gaba da kare ribar da aka samu ta hanyar ba da muhimmanci ga tsaro da ababen more rayuwa.
Sanwo-Olu ya kuma jaddada ƙoƙarin jihar wajen ƙarfafa kuɗin shiga na cikin gida (IGR) ba tare da cika wa al’umma nauyi ba, sannan ya yi kira ga Majalisar Kasuwanci ta ci gaba da shiga cikin tattaunawa kan manufofi, saka jari a al’umma, da kuma ɗaukar nauyin al’umma.
Gwamnan ya yaba wa Sarki Oniru na ƙasar Iru, Abdulwasiu Lawal, saboda kafa dandalin da ke haɗe al’adu da kasuwanci, inda ya ce mulkin gargajiya da shugabancin kwarai sun samar da ingantaccen yanayi na zuba jari da ci gaban birni mai tsari.
“Ci gaban yankin Oniru shi kansa labari ne mai ƙarfi. Abin da da yawa aka ɗauka a matsayin yankin zama kawai, yanzu ya zama cibiyar harkokin kasuwanci, masaukin baki, gine-gine, da ƙere-ƙere,” inji gwamna.
Ya ƙara da cewa, haɗin kai tsakanin al’adu da ci gaba na samar da tushe mai ƙarfi don ci gaba mai ɗorewa, tare da jaddada cewa Legas ta zama cibiya ta Afirka wacce ke jan hannun jarin duniya, tare da ƙarfafa basirar gida.
Sanwo-Olu ya bayyana shirye-shiryen ƙaddamar da Iru Business Network da kafa Oniru Business Council a matsayin dandalin haɗin kai mai ɗorewa. Wannan zai taimaka wajen bibiya, lura da ci gaba, da tabbatar da gaskiya a harkokin kasuwanci, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kasuwanci, al’umma da gwamnati.
Gwamnan ya kuma jaddada buƙatar haɗin kai da zaman lafiya, inda ya ce haɗin kai tsakanin fadar sarki da al’umma zai haifar da zaman lafiya, bambanci da kuma ƙarfin aiki da zai jawo ci gaba ga kowa da kowa.
