Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta sanar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu da kashi 15.10 a watan Janairun bana, lamarin da ke nuna alamun samun sauƙi daga tsadar rayuwa da aka daɗe ana fama da ita.
Wannan sauyin ya faru ne sakamakon daidaita tsarin lissafin da hukumar ke amfani da shi domin ya dace da yanayin kasuwanci a ƙasar.
Hakan ya sa farashin kayayyakin ya ragu idan aka kwatanta da kashi 27.61% a bara.
Shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa wannan raguwa ta faru ne sakamakon sabon tsarin lissafi daga salon kasuwanci na shekarar 2024.
Wannan sabon tsarin ya sa alƙaluman hauhawar farashi sun yi ƙasa, amma kamar yadda masana suka yi gargaɗi, wannan ba yana nufin farashin dukkan wasu kayayyaki ya riga ya karye a kasuwanni ba.
