Dole a zamanantar da tsarin haraji – Shugaban NRS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Tara Haraji ta ƙasa (NRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cewa nasarar aiwatar da sabbin dokokin sauya fasalin haraji a Nijeriya za ta ta’allaƙa ne kacokan kan rungumar tsarin fasahar zamani mai dogaro da bayanai da na’urori masu aiki kai tsaye.

Adedeji ya yi wannan jawabi ne a wani taro mai taken “Daidaita Tsarin Tara Haraji da Aiwatar da Sabbin Dokokin Haraji,” wanda FCT Internal Revenue Service (FCT-IRS) ta shirya a Abuja.

Ya jaddada cewa duk da cewa dokokin sauya fasalin haraji na 2025, da suka fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, sun samar da tubalin doka domin gina tattalin arziki mai adalci, ba za su yi tasiri ba idan aka ci gaba da tafiyar da su ta hanyar takardu da tsari na gargajiya.

Shugaban NRS, wanda Babban Sakataren Joint Taɗ Board, Olusegun Adesokan, ya wakilta, ya ce sauyawa zuwa “basirar haraji” ce kaɗai za ta bai wa ƙasa damar cimma burin tara naira tiriliyan 40.71 a shekarar 2026 ba tare da ƙara wa ‘yan ƙasa haraji ba.

A cewarsa, gyaran tsarin kuɗi da haraji na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nufin sake fasalta tsarin kuɗaɗen shiga na cikin gida, amma nasarar hakan za ta dogara ne kan yadda jihohi da ƙananan hukumomi za su aiwatar da su yadda ya kamata.

Ya yi gargaɗin cewa rarrabuwar kawuna a aiwatar da manufofi na iya raunana gyara, yayin da haɗin kai tsakanin hukumomi zai ƙarfafa shi. A cewarsa, kasancewar Abuja cibiyar ƙasa, dole ne ta zama abin koyi wajen nuna gaskiya da tafiyar da al’amura cikin zamani.

Adedeji ya nuna damuwa kan matsalolin da ke addabar tsarin tara haraji, ciki har da yawaitar haraji iri-iri, hanyoyin tara kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, shingayen hanya na haram da sayar da tambari da laƙabi ba tare da tsari ba. Ya ce irin waɗannan halaye na ƙara tsadar kasuwanci tare da rage amincewar jama’a ga gwamnati.

Ya ba da shawarar kafa haɗaɗɗen tsarin aiki tsakanin Hukumar Babban Birnin Tarayya, FCT-IRS da ƙananan Hukumomi, tare da fayyace ayyuka, raba bayanai da kafa tsari guda na bin doka, domin kauce wa maimaituwa da sauƙaƙa wa masu biyan haraji.

A ɓangarensa, Muƙaddashin Shugaban FCT-IRS, Michael Ango, ya ce manufar daidaita tsarin ba wai kwace hurumin wasu hukumomi ba ne, illa samar da inganci wajen tara kuɗaɗen shiga. Ya ce kuɗaɗen za su ci gaba da zuwa inda kundin tsarin mulki ya tanada, amma ana son kafa tsarin yanar gizo guda ɗaya da zai sauƙaƙa biyan haraji a Abuja.

Ango ya ƙara da cewa burin su shi ne samar da kuɗaɗen da za su tallafa wa gina tituna, asibitoci, makarantu da sauran ababen more rayuwa, musamman ma yayin da ake cika shekaru 50 da ƙirƙiro Abuja a 1976. Ya kuma nuna cewa aiwatar da sauye-sauyen haraji a matakin cikin gida zai dogara ne kan yadda majalisar dokoki za ta tsara jadawalin aiki.

By ukarofi