Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta bayyana cewa tsarin sayar da kamfanonin wutar lantarki a Nijeriya ya kasance “babban zamba”.
A yayin wani taron shekara-shekara na mata da matasa na ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta ƙasa (NUEE) da aka gudanar a Abuja a ƙarshen mako, Shugaban NLC, Kwame Joe Ajaero, ya bayyana cewa fiye da shekaru goma bayan rarraba sashen wutar lantarki, samar da lantarki ya tsaya ne tsakanin megawatt 4,000 zuwa 5,000, wato daidai matakin da ake da shi kafin tsarin sayarwar.
Ajaero ya ce: “Shekaru goma bayan sayarwar da aka yi wa duniya tamkar babban nasara, me muka samu? Maimakon ci gaba, muna ganin koma baya. Maimakon haske, muna cikin duhu. Babban tushen lantarki na ƙasa na rushewa akai-akai, wani lokaci yana sanya ƙasar gaba ɗaya cikin rashin lantarki. Wannan ba shi ne sauyi da aka yi alƙawari ba; wannan babban satar dukiyar talakawa ce.”
Ya zargi kamfanonin rarraba wuta da ƙin karɓar lodin da aka ware musu daga Kamfanin Kula da Wutar Lantarki na ƙasa (TCN), yayin da talakawa ke fama da katsewar wuta da hauhawar farashi.
Shugaban NLC ya ce sayar da kamfanonin da suka gaji da PHCN ga masu zuba jari ba tare da ƙwarewar fasaha ko ƙarfin kuɗi ba, babbar zamba ce ta miƙa dukiyar jama’a ga ‘yan kasuwa.
Ya ce: “Masu zuba jari ba su kawo sabbin kuɗi ba cikin ƙasar nan. Sun aro kuɗi daga bankunan Nujeriya, suna rage bashin gida, kuma suna ƙara matsin lamba a kan Naira. Sun sayi kamfanonin lantarki da GENCO kan kuɗi kaɗan, yanzu suna son ma’aikata su biya bashin su ta hanyar hauhawar farashin lantarki.”
Ajaero ya kuma soki tsarin amfaninda lantarki na Bands A, B, da C bisa ga sa’o’in amfani da wuta, inda ya ce ya zama wata hanyar ƙara farashi a ɓoye.
Game da shirin gwamnatin tarayya na biyan Naira tiriliyan 2 zuwa tiriliyan N3 ga kamfanonin samar da wuta a matsayin bashin tallafi, Ajaero ya ce babu hujja da ke goyon bayan wannan kashe kuɗi ga kamfanonin masu zaman kansu da suka kasa samar da wuta yadda ya kamata.
Ya ce: “Bashin tallafin lantarki ba shi da tushe. Tiriliyan N3 da ake maganar wani yaudarar ce kawai kuma ba ta zuwa ko ina. Muna kallon wannan a matsayin wani shiri na biyan ‘yan ɓoye-ɓoye yayin da za a yi zaɓe a 2027. Kowane kobo na kasafin ƙƙsa na ma’aikata da talakawa ne.”
Ya ce duk da cewa Sabon Dokar Wutar Lantarki ta baiwa jihohi ikon samar da wuta da rarraba ta, rarrabuwar kanta ba zai magance matsalolin tsarin ba.
Ajaero ya kira taron ƙasa na masu ruwa da tsaki, ciki har da ƙungiyoyin ma’aikata, masana’antu, da kwararru don samar da abin da ya kira “Taswirar Wutar Jama’a”, wanda zai mayar da hankali kan samar da wuta mai araha kuma tsayayya, saka hannun jari na gwamnati a samarwa da watsa wuta, farashin da ya dace da aiki, da dawo da tsarin sayarwar wutar zuwa hannun jama’a.
Ya ƙara da cewa: “Talakawan Nijeriya ba za su ci gaba da biyan kuɗi sannan su zauna a duhu ba. Idan wuta ba ta samuwa ba za ta kasance mai araha ba.”
