Tinubu da shugaban UBA sun tattauna sauye-sauyen haraji da ƙarfafa ƙananan sana’o’i

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban rukunin bankin United Bank for Africa (UBA), Tony Elumelu, domin tattauna hanyoyin bunƙasa tattalin arziki, sauye-sauyen haraji da kuma ƙarfafa ƙanana da matsakaitan sana’o’i (SME) a Nijeriya.

Ganawar ta gudana ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda Elumelu ya bayyana wa manema labarai cewa tattaunawar ta fi mayar da hankali kan yadda za a ƙara tallafa wa ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa, waɗanda ya bayyana a matsayin “injin ci gaban tattalin arziki.”

A cewarsa, Shugaba Tinubu na da matuƙar sha’awa wajen ƙarfafa gwiwa da bai wa masu ƙananan sana’o’i damar bunƙasa harkokinsu, musamman matasa masu tasowa a fannin kasuwanci. Ya ce shugaban ya nuna cikakken goyon baya ga shirye-shiryen da za su taimaka wajen ba su jarin ilimi, kuɗi da tsari mai kyau.

Elumelu ya ƙara da cewa, sauye-sauyen haraji da ake aiwatarwa a halin yanzu za su kasance wata muhimmiyar hanya ta faɗaɗa damar kasuwanci da ƙarfafa ƙananan kasuwanci. Haka kuma, an tattauna batun Bankin Masana’antu (BOI), inda shugaban ƙasa ya nuna gamsuwa da yadda shugabancin bankin ke tafiyar da ayyukansa.

Ya bayyana cewa haɗin kai tsakanin gwamnati da ɓangaren masu zaman kansu abu ne mai ƙarfafa gwiwa, musamman ga matasan Nijeriya da ke neman kafa sana’o’i. Ya kuma yi wa shugaban ƙasa bayani kan yadda yake kallon yanayin tattalin arzikin ƙƙsar a yanzu.

Dangane da manufofin kuɗaɗe, Elumelu ya ce alƙiblar manufofin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na da kwarin gwiwa, tare da nuna cewa ana samun daidaito da tsari mafi kyau idan aka kwatanta da baya. Ya kuma ce matsalar samun kuɗin waje (foreɗ) ba ta da tsanani kamar yadda take a lokutan baya.

A ɓangaren wutar lantarki, ya ce an tattauna muhimmancin inganta samar da wuta domin bunƙasa tattalin arziki. A cewarsa, Shugaba Tinubu ya nuna aniyar hanzarta biyan basussukan da ake bin gwamnati a ɓangaren wutar lantarki domin kamfanonin samar da wuta su ƙara yawan samarwa.

Elumelu ya gode wa shugaban ƙasa bisa jajircewarsa wajen tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa, aarfafa matasa da kuma farfaɗo da ɓangaren wutar lantarki domin haɓaka tattalin arzikin ƙasa.

By ukarofi