Makwabta sun hallaka matashi bayan zargin afka wa mahaifiyarsa da adda

Spread the love

Wani matashi mai shekara 16 ya rasa ransa a Abuja bayan da ake zargin wasu makwabta sun doke shi har lahira, bayan ya far wa mahaifiyarsa da adda yayin wata taƙaddama ta cikin gida.

Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga Fabrairu, 2026, a unguwar Byazhin, Kubwa, cikin ƙaramar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fara ne a matsayin saɓani tsakanin matashin da mahaifiyarsa kafin daga bisani ya rikiɗe zuwa ramuwar gayya daga wasu mazauna unguwar.

A cewar rundunar ’yan sanda, Hedikwatar ’Yan Sanda ta Byazhin ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:45 na dare cewa wani matashi mai suna Chidera ya kai wa mahaifiyarsa hari da adda yayin wata taƙaddama. Nan take jami’ai suka isa wurin.

Binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga zargin cewa matashin yana tura kuɗi daga asusun bankin mahaifiyarsa zuwa asusunsa na Opay ba tare da izininta ba. Lokacin da ta fuskance shi kan lamarin, ana zargin ya fusata tare da kai mata sara da adda a hannu.

’Yan sanda sun ce wasu makwabta biyu, Cosmos Okafor mai shekara 31 da Okechukwu Wisdom mai shekara 17, sun shiga tsakani bayan sun ga abin da ke faruwa. Sai dai ana zargin su biyun sun kai wa matashin hari a martani ga abin da ya yi wa mahaifiyarsa.

A yayin dukan, Chidera ya samu munanan raunuka kuma ya suma. An garzaya da shi Asibitin Kubwa General Hospital inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

An kama mutanen biyu da ake zargi kuma suna tsare a hannun ’yan sanda yayin da ake ci gaba da bincike.

Kwamishinan ’Yan Sanda na FCT, Miller G. Dantawaye, ya jajanta wa iyalan mamacin tare da gargaɗin al’umma kan ɗaukar doka a hannu.

Kakakin rundunar ’yan sandan FCT, Josephine Adeh, ta bayyana cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Rundunar ta kuma buƙaci mazauna yankin da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ke tayar da hankali ta hanyoyin kiran gaggawa domin hana faruwar irin waɗannan munanan al’amura a nan gaba.

Lamarin ya sake tayar da muhawara kan matsalar ɗaukar doka a hannu, wato mob justice, da ke ci gaba da faruwa a sassa daban-daban na ƙasar nan.

By ukarofi