
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Mainagge Arewa Cultural Group Limited ta yi jimamin rasuwar marigayi Malam Nura Shariff na Kamfanin Abnur Entertainment.
Ta ce, rasuwar marigayin babban rashi ne ga iyalansa da sauran makusantansa da kuma harkar finafinai baki ɗaya.
A wata takarda daga Abdullahi Rabi’u Jikas, ƙungiyar ta bayyana Nura Shariff a matsayin jajirtacce, mai kawar da kai da kuna son aikinsa, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa ga ci-gaban masana’antar finafinai ta Kannywood.
Ta kamfaninsu na Abnur Entertainment, Shariff ya taimaka wajen haskawar taurari masu tasowa da dama, samar da damarmaki da kuma barin horon da ya shafi aiki tuƙuru, ƙirƙira da kasancewa cikin aiki a kodayaushe, tana mai cewa kirki da hikimominsa za su cigaba da zama ababen tunawa da koyi.
A ƙarshe, Mainagge Arewa Cultural Group ya yi addu’ar fatan Allah ya jiƙan sa ya kuma gafarta masa, tare da bada haƙurin juriyan rashinsa ga iyalai da makusantansa.


