Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta ƙi sauraren ƙorafin belin El-Rufa’i, ta ɗage shari’ar zuwa 23 ga Afrilu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Laraba Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama a Abuja, ta ƙi amince wa sauraron ƙorafin nema belin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya shigar mata, inda ta bayyana hakan a matsayin abin da “bai nuna ba” sannan ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Afrilu, 2026.

Mai Shari’a, Joyce Obehi Abdulmalik ne ya yi hukuncin.

A cewar ShaharaReporters, kotun ta ƙi bai wa lauyoyin El-Rufa’i dama su gabatar da shari’ar a yayin zaman na yau Laraba.

Haka kuma, an gano cewa tsohon gwamnan baya nan a lokacin zaman kotun kasancewar yana hannun Hukumar Yaƙi da Laifukan Rashawa, ICPC.

Sannan wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa ta ADC kamar su Bolaji Abdullahi, sun samu halartar zaman domin ganin yadda shari’ar ke gudana.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da rikicin shari’o’i da suka haɗa tsohon gwamnan da hukumomin yaƙi da rashawa.

Da fari, El-Rufa’i ya shigar da ƙarar neman biyan sa tarar biliyan N1 akan ICPC da wasu ɓangarori uku bisa abin da ya kira da “kutse a gidansa na Abuja ba bisa doka ba.”

El-Rufa’i, wanda tsohon ɗan jam’iyyar APC ne, ya koma ADC, sannan ya ci alwashin jagorantar haɗakar da take neman tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu bai koma fadar Aso Rock ba a zaɓen 2027.

By Babaji