An ci tarar Chelsea da West Ham kan hatsaniya tsakanin ’yan wasa

Spread the love

An ci tarar Chelsea fam 325,000 da kuma West Ham fam 300,000, sakamakon wani rikici da ya ɓarke tsakanin ’yan wasa karawar da suka yi a Premier League a watan Janairu a Stamford Bridge.

Lamarin ya faru ne a minti 95, inda ɗan wasan Chelsea, Joao Pedro ya ƙalubalanci Adama Traore na West Ham, saboda ture Marc Cucurella da ya yi.

Bayan da aka duba VAR, sai alƙalin wasa Anthony Taylor ya bai wa Jean-Clair Todibo jan kati kai tsaye saboda shake wuyan Joao Pedro da ya yi.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta bayyana cewa Chelsea da West Ham sun kasa tsawatar wa a lokacin yamutsin.

Tun farko dukkan ƙungiyoyin sun amince da tuhumar da aka yi musu.

Dukkan ƙungiyoyin biyu sun amince da laifin da ake tuhumarsu da shi.

By ukarofi