Gwamnan Sakkwato ya buƙaci masu hali su riƙa ciyar da masu azumi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnan jihar Sakkwato Ahmed Aliyu ya yi kira ga masu hannau da shuni a jihar su taimaka wajen cikyar da mabuƙa a faɗin jihar.

Gwamnan ya yi kirane ne a lokacin da ya kai ziyara wata cibiyar da gwamnatinsa ke ciyar da masu azumi.

Ya ce gwamnatinsa na bayar da tallafin abincin buɗe-baki ga masu azumi a jihar, wanda ya ce za a riƙa bai wa aƙalla masu azumi 34,000 a kullum.

A lokacin ziyarar, gwamnan ya ziyarci cibiyoyin da ke titin Clapperton da Lodge Road da Gidan Dallatu da asibitin ƙwararru da yankin Madunka, inda ya yaba da ingancin abincin da ake rabawa ga mutane.

“Na yaba da ingancin abincin, da kuma irin yadda ake zuba wa mutane isasshen abinci. Duk wuraren da na ziyarta, na gamsu da aikin da suke yi,” in ji gwamnan.

Gwamnan ya ƙara da cewa an samu ci gaba a irin ingancin abincin a bana, idan aka kwatanta da irin abincin da aka raba a shekarar da ta gabata.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin masu aikin ciyarwar, waɗanda ya ce suna matuƙar ƙoƙari. “Mun ƙirƙiri ciyarwar nan ne domin sauƙaƙa wa marasa ƙarfi domin su samu sauƙin yin buɗe-baki. Don haka ina kira ga kwamitin abincin su ƙara ƙaimi,” in ji shi.

Ahmad Aliyu ya yi alƙawarin ci gaba da ba ciyarwar azumi muhimmanci a gwamnatinsa.

Ya ce gwamnatin jihar ta ware naira biliyan 1 domin ciyarwar azumin bana, inda ya ce kullum za a ciyar da mutum 34,000 ne.

By ukarofi