
Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da hare-haren soji akan Iran, inda Shugaban Amurka, ya tabbatar da cewa an fara manyan ayyukan fada a yankin.
Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da cewa Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-haren ramuwar gayya, lamarin da ya kara dagula yanayin tsaro a Gabas ta Tsakiya.
Hotuna da bidiyo da ke yawo sun nuna hayaki na tashi a sararin samaniyar birnin Iran, yayin da aka ji karar fashe-fashe a birane biyar na Iran.
Shugaba Trump ya kuma yi kira ga al’ummar Iran da su “kwace mulkin kasarsu,” yana mai cewa wannan na iya zama dama ta musamman da ba za ta sake samu wa ba a cikin dogon lokaci.
A kwanakin baya, Washington ta kara matsa lamba kan Tehran domin amincewa da sabuwar yarjejeniya kan shirinta na nukiliya. Trump ya bayyana a ranar Juma’a cewa bai gamsu da matsayin Iran ba a tattaunawar da ake yi kan batun nukiliya.
Rahotanni daga yankin sun ce har yanzu Isra’ila na tuna yakin kwanaki 12 da ta yi da Iran a watan Yunin da ya gabata, wanda ya janyo mummunar illa ga tsarin kariyar sararin samaniyar ta.
