Kaduna: Gobara ta tashi a fadar Sarkin Jama’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Juma’a ne gobara ta ƙone wani sashi na fadar sarki a Kafanchan, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna, lamarin da ya jafe al’ummar yankin cikin firgici.

Gobara ta ƙone sashin fadar ne,wadda mai martaba sarkin Jama’a, Alhaji Dokta Muhammad Isa Muhammad ke jagoranta.

Rahotanni da hotuna sun tabbatar da cewa gobarar ta kama ne da yamma, inda jama’a suka kai ɗauki domin kashe ta.

Saidai jami’an tsaro sun hana cincirindon mutanen da suka yi niyyar ƙarasawa saboda halin rashin tabbas, da kuma bai wa ƙwararrun masu kashe gobara damar yin aikinsu yadda ya kamata.

Kawo lokacin haɗa wannan labarin babu cikakken bayanin abin da ya yi sanadiyyar tashin gobarar da kuma irin ɓarnar da ta yi.

By Babaji