
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Jihar Oyo ta tabbatar da sahihancin babban taron Jam’iyyar PDP da aka yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025 a Ibadan, inda aka zaɓi sabon shugabancin Jam’iyyar.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Ladiran Akintola, ya ce taron da zaɓukan sun cika dukkan sharuɗɗa da ka’idojin da dokokin ƙasa da na jam’iyyar suka tanada.
Kotun ta kuma ƙaryata dukkan buƙatun da wasu suka gabatar waɗanda ke ƙalubalantar taron, ciki har da neman dakatar da sakamakon taron, inda ta ce ba su da tushe.
Hukuncin ya umurci INEC da ta amince da sakamakon taron, ciki har da jagorancin Dakta Kabiru Tanimu Turaki a matsayin sahihin shugabancin jam’iyyar.
Saidai wasu ɓangarorin PDP, musamman ƙarƙashin haɗin-gwiwar Nyesom Wike, sun bayyana wannan hukunci a matsayin maras tasiri, inda suka ce umarnin Babbar Kotun Tarayya da ta dakatar da taron ya fi ƙarfi.
A yanzu dai rikicin na cigaba, yayin da ake jiran hukuncin ƙarshe daga Kotun Ƙoli matuƙar ɗaya tsagin ya ɗaukaka ƙara.
