Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
DCP Aminu Usman Gusau na sashin kuɗi ya wakilci kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Bello Shehu inda ya miƙa cekin kuɗin ga iyalan jami’an yan sandan da suka rasa rayukansu a yayin da suke gudanar da aikin su.
Wannan kuɗi Naira miliyan 32 da dubu ɗari biyu da aka raba wa iyalan mamatan sun fito ne ƙarƙashin shirin Inshora na mutuwa ko raunuka da ya shafi duk wani ɗan sanda a lokacin da yake aiki.
A jawabinsa CP Bello Shehu ya yabawa babban sufeton ‘yan sanda na ƙasa Ag.IGP Olatunji Rilwanu Disu kan yadda ya nuna tausayinsa ga iyalan yan sandan da suka rasa rayukansu a lokacin da suke wa ƙasa aiki.
Sai ya hori iyalan mamatan da su tabbatar sun yayi amfani da kuɗaɗen wajan kyautata rayuwar iyalin su kamar yadda shirin Inshora ya tsara na samar da mafita ga iyalai da mamatan suka bari.
CP Bello Shehu yayi addu’ar Allah ya jiƙan mamatan da rahama, ya raya abinda suka bari.
Hamza Surajo wanda yayi magana a madadin iyalan mamatan ya gode wa AIG DISu bisa ƙoƙarin da yayi na ganin sun sami haƙƙoƙin su ya tabbatar da cewa za su yi amfani da waɗannan kuɗaɗen wajen ɗawainiyar mamatan.
