
Shugaba Donald Trump na Amurka ya buƙaci Iraniyawa su yi amfani da manyan hare-haren Amurka da Isra’ila wajen kifar da gwamnatin ƙasar.
A cikin wani jawabi da ya yi ta bidiyo, Mista Trump ya ce ”Idan muka gama namu, ku kuma ku ƙwace gwamnatin, taku ce, ina ganin wannan ce damar da kuka samu ta yin hakan”.
Ya kuma faɗa wa dakarun sojin Iran cewa za a ba su ”kariya” idan suka amince su ajiya makamansu, ko kuma su ”fuskanci mutuwa”.
A farkon watan Janairu ne Trump ya yi barazanar kai harin bom kan Iran saboda yadda jami’an tsaron ƙasar ke far wa masu zanga-zangar adawa da gwamnati.
Al’amarin ya sa ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta ce an kashe aƙalla mutane guda 6,480.
