Iran ta yi ruwan wuta akan sojin Amurka da ke Ƙatar, Bahrain da wasu ƙasashe

Spread the love

Rahotanni sun nuna cewa ƙasar Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya akan sansanonin sojojin Amurka da ke wasu ƙasashen yankin gabas ta tsakiya.

Hakan na nufin mayar da martani ga hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai mata da safiyar yau Asabar.

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila, IDF ta fitar, ta tabbatar da gano makamai masu linzami da Iran ta harba cikin Isra’ila, amma tana ƙoƙarin ganin ta kakkaɓo su.

Haka ma Qatar ta tabbatar da cewa Iran ta kai hari kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke ƙasaer, kodayake ta ce an kakkaɓo hare-haren.

Ita ma ƙasar Bahrain ta tabbatar da kai hari kan sansanonin sojin ruwan Amurka da ke ƙasar, kodayake ba ta alaƙanta harin da kowace ƙasa ba.

By Babaji