
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sufeto Janar na Rundunar ‘yan sanda na riƙo, Olatunji Disu ya tsige ACP Bukola Kuti a muƙamin Babbar Jami’a mai daraja ta 2 (PSO2) ta jami’ai a lokacin tsohon Sufeto Janar Kayode Egbetokun, inda ya mayar da ita Cibiyar Nazarin Tsare-tsare da Dabaru ta Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru.
Majiyoyi da dama daga rundunar sun tabbatar wa jaridar ShaharaReporters cewa sauyin zai fara aiki ne a nan take, wanda ya haddasa cece-kuce acikin manyan jami’an ‘yan sanda musamman bisa la’akari da makomar matsayinsu.
ACP Kuti ta yi aiki ne a matsayin PSO2 ga Egbetokun, muƙamin da ke da girman daraja acikin aikin ‘yan sanda.
Ba ta matsayin da ƙara mata girma da aka yi a baya ya janyo faɗi-in-faɗa musamman ganin yadda ake sukar matakin a tsakanin manyan jami’an rundunar.
A cewar ShaharaReporters, ɗaukakar Kuti da samun kusanci da tsohon shugaban ‘yan sandan su suka haifar da saɓani a ciki da wajen rundunar.
Wasu na ganin matakan da sabon jagoran ya ɗauki akan jami’ar daidai ne wajen yunƙurin samar da gyara a harkokin gudanarwa, yayin da wasu ke fassara hakan da ƙoƙarin rage ƙamarin fargaba da saɓani acikin jami’an.
A shekarar 2012 Kuti ta fada aiki da rundunar ‘yan sandan Nijeriya. Duk da cewa akwai waɗanda suka riga ta shiga aikin da shekaru takwas zuwa goma, amma ta samu ɗaukaka sama da su cikin ƙanƙanin lokaci.
Ana raɗe-raɗin cewa a yanzu tana dab da samun muƙamin mataimakin kwamishina mai daraja ta ɗaya, wato DCP, lamarin da ya ƙara tayar da cece-kuce acikin manyan jami’ai da ke ganin hakan a matsayin barazana ga gaskiya da adalci a harkar ƙarin matsayin a hukumar.
