Harin Iran ya tarwatse a filin jiragen saman Dubai da Burj Al Arab

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

​Rahotanni daga yankin Gabas ta Tsakiya sun bayyana cewa an sake jin ƙarar fashe-fashe masu ƙarfi a sararin samaniyar biranen Dubai (UAE) da Doha (Qatar) a yau Lahadi.

Wannan shi ne rana ta biyu a jere da yankin ke fuskantar hare-hare tun bayan kisan shugaban Iran, Ali Khamenei.

Mazauna biranen sun ce sun ji ƙararrakin da suka girgiza gine-gine, wanda ake kyautata zaton na kakkaɓo makaman linzamin Iran ne da tsarin kariya na kasashen ke yi.

An tabbatar da cewa harin daren jiya ya janyo gobara a tsibirin Palm Jumeirah da kuma ɓarna kaɗan a filin jirgin saman Dubai (DXB), inda mutane hudu suka jikkata.

A birnin Doha, wasu makaman sun fada kusa da unguwannin mazauna, inda mutane takwas suka samu raunuka.

​Tuni dai manyan kamfanonin jiragen sama irin su Emirates da Qatar Airways suka dakatar da zirga-zirga har sai zuwa ƙarfe 3 na rana.

​Gwamnatin UAE ta fitar da saƙon gaggawa ga mazauna ƙasar da su nemi mafaka kuma su nisanci wuraren da ake da fargabar hari akansu.

By Babaji