
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan bindigar da suka yi awon-gaba da Sarkin ƙauyen Ndufu-Alike, Ezeogo Francis Igwe na Ƙaramar Hukumar Ikwo ta Jihar Ebonyi, sun halaka shi.
Rahotanni sun bayyana cewa, Sarkin, wanda mahaifi ne ga tsohon mataimakin gwamnan jihar, Kelechi Igwe, an yi garkuwa da sh ien a ranar 1 ga watan Maris, 2026.
Al’amarin ya faru ne a lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki akan babura a ƙauyen, inda suke yi garkuwa da shi tare da tafiya da shi zuwa wani wajen da ba sani ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Joshua Ukandu, ya bayyana cewa an kashe sarkin ne kwana guda da sace shi.
Ukandu ya ce bayan garkuwa da sarkin ne, jami’an hukumar suka gaggauta ƙaddamar da atisayen ceto shi.
Kakakin ya ƙara da cewa, a yayin atisayen, ‘yan sanda sun yi nasarar kama mutane biyu da ake zargin suna daga cikin ‘yan bindigar da sukar sace sarkin.
A yayin bincike ne mutane biyun suka tabbatar da mutuwar sarkin tun a ranar 2ga watan Maris. Haka kuma sun jagoranci jami’an zuwa maɓoyar ‘yan bindigar wajen gano gawar marigayin.
Kazalika, Ukandu ya ce sai da aka yi ba-takashi tsakaninsu da ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu tserewa saboda ƙarfin makaman jami’an akan nasu.

