Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 45 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wata takarda ɗauke da sa hannun kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa, ya bayyana cewa cikin ‘yan bindigan da sojojin suka kashe har da babban kwamandan ‘yan bindigan Adamu Alieru.

Haka kuma Sojojin sun sami nasarar kashe Alti wanda shine mataimakin kwamandan ‘yan bindigan kuma ɗan’uwa ga Adamu Alieru da Damale shima ɗaya daga jagororin ‘yan bindigan.

A cewar kwamishinan ɓangaren sojoji Kaftin Paul Hassan da wasu mutum biyu suka rasa ransa a ɗauki ba daɗi da sojojin suka yi da ‘yan bindigan a ƙaramar hukumar Ɗanmusa.

Ya ce tun da farko, ‘yan bindigan ɗauke da manyan makamai akan babura da suka fito daga jihar Zamfara suka shiga ƙauyen Alhazawa a ƙaramar hukumar Musawa domin aikata ta’addanci amma a cewar sa jami’an tsaron CWC haɗin gwiwa da tubabbun ‘yan bindiga a yankin suka fatattake su.

Jami’an tsaron suka kashe yan bindiga huɗu tare da ƙwato dabbobi da ‘yan bindigan sukai ƙoƙarin awon gaba da su.

Dr Nasiru Ɗanmusa ya bayyana cewa bayan da suka sake dawowa domin ɗaukan fansa sai dai akan hanyar su ta zuwa Musawa suka ci karo da sojojin sansanin Ɗan Ali da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa.

Nan ne sojojin su kai ta ɗauki ba daɗi da yan bindagan da yayi sanadiyar mutuwar kaftin Paul Hassan da wasu sojoji biyu,yan bindiga 45 wajen faɗan sojojin suka kashe.

Kwamishinan ya ce tuni gwamna Dikko Raɗɗa ya mika ta’aziyar sa ga rundunar sojoji da iyalan sojojin da suka rasa rayukansu.

“Dikko Raɗɗa ya jinjina da sojojin kan yadda suka sadaukar da rayuwar su da nuna ƙwarewa wajen yaƙar ‘yan bindigan,”Inji Dr Ɗanmusa.

Kwamishinan ya tabbatar wa al’ummar jihar Katsina cewa gwamnati za ta cigaba da yaƙar yan bindiga a duk inda suke har sai sun kakkaɓe su faɗin jihar Katsina.

By ukarofi