POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi wajen kasuwanci da fitar da kuɗaɗe da tura su

Spread the love

Daga FARFESA AHMAD MURTALA

Bismillahir rahmanir rahim. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Annanbinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa bakiɗaya.

Bayan haka, a yau Laraba 23 Jumada Ula, 1442 H.-06 Janairu, 2021 M., na sami tambaya ta fuskoki da yawa har sai da aka rubuto cewa: “Malam ana cikin bukatuwar yin cikakken bayani a dangane da POS. Wasu malaman sun haramta, wasu kuma sun halatta, Mun gode”. Wannan ita ce tambayar. Amma jin akwai wannan sabani na malamai a nan Kasar, ya sa na yi kamar ba zan bada amsa ba. Saboda ban cika son shiga irin mas’alolin da aka sami karakaina ba, ba tare da na na ji ko na karanta abin da kowane bangare ya fada ba. Sai dai tambayar ta zo daga wajen wani mutum mai kima a idona. Don haka na rubuta wannan bayani. Amma ba wai na rubuta ba ne a matsayin dole sai na gamsar da kowa da kowa ba. Wannan ba zai taba yiwuwa ba. Na dubi mas’alar ne da kyau gwargwadon abin da Allah ya huwace a yanzu-yanzu. Allah ya bamu sa’a da dacewa.

1- Yana da kyau a rika sanin tarihin wasu abubuwa da yadda suka taso da yadda suke amfani da sauran wasu abubuwan da suka shafesu. Saboda ta haka ne za a iya basu hukuncin da ya dace da su a Shar’ance. Imamu Shafi’i yana cewa, “Na dauki lokaci ina karanta ilimin tarihi, shekara kaza da kaza! Amma na karantashi ne kurum don na taimaka da shi wajen fahimtar ilimin Fikihu”.

2- Akan haka, bari mu fara da dan tarihi kadan. Abin da ake nufi da PoS shi ne ‘Point of Sale’ “نقاط البيع” . A wani lokacin kuma ana kiransa da sunan POP wato Point of Purchase. Duka biyun a asalinsa suna nufin tsarin kididdige cinikin da mai kanti ya yi a nan take ba tare da wata wahala ba. An fara kirkiro tsarin POS tun a 1879 M. Da sunan ‘Cash Register’. Sunan wanda ya fara kirkiroshi James Ritty. Yana da babban shago kayan masarufi. Amma sai ya fahimci ma’aikatansa suna yi masa dingushe. Don haka sai ya sa aka kirkiro inji da sunan ‘Incorruptible Cashier’ don ya rika sanin adadin abin da ya shigo lalitarsa. A 1906 M. a ka fara jona wannan inji da wuta, ta yadda ya kara sauri wajen aikinsa. Sai kuma a shekarun 1970s aka fara hada wannan fasaha da na’ura mai kwakwalwa. Haka ya wanzu har shekarun 1990s a inda aka fara kera injina na zamani, wadanda su da kansa kwanfiyuta ne. Shegowar shekarun 2000s a nan ne aka fara samar da irin wadannan injin amma wadanda za a iya dauka a hannu daga nan a kaisu can, suna kiransu da ‘mPOS’ -wato Mobile POS.   

3- Tsarin POS ya shigo Nigeria sosai  2012 M. a lokacin da Babban Bankin Tarayya ya huwacewa ‘yan kasa su rika amfani da shi saboda rage zirga-zirga da kudade a hannu. Kafin haka kaso 90% na cinikayya ana yinsu da kudade a hannu tsirara! –(Challenges to the Efficient Use of Point of Sale (POS) Terminals in Nigeria na Adeoti).

4- Akwai POS kala-kala wanda kamfanoni da wuraren sayar da abinci da abin-sha da otel-otel suke amfani da su. Kowanne yana neman wanda ya dace da bukatarsa. Amma amfani da POS a matsayin wurin da za a iya zuwa a nemi su baka wani gwargwado na kudi, su kuma su yi amfani da katin mutum na ATM su dibi wannan kuɗin su tura zuwa ‘account’ ɗinsu a maimakon wanda suka bashi a nan take, wannan ya fara ne a ‘yan shekarun nan, ba da dadewa ba. 

5- Kafin mutum ya bude wurin harkar POS sai ya bi wasu matakai kamar haka:

i- A dokokin Kasa an yarda a bude irin wadannan wurare kamar yadda aka fada a baya.

ii- Masu harkar POS suna da alaka da bankuna ta fuskar sai sun je sun yi rijista da wani banki tukuna. Daga cikin hikimomin yin haka shi ne don bankin zai ga ana hada-hadar kudade masu yawa akai-akai, sai ya zamo ba zai damu ba, saboda ya yarda da ‘account’ ɗin da ake wannan hada-hadar da shi.

iii- Akwai certificate da bankin zai bawa wanda ya yi rijista da shi a matsayinsa na “agent”-wakilinsu. Don haka zai yi rawa da bazar wannan bankin a iya bangaren da suka yarjewa POS ya yi hidima. 

vi- Bankin da aka yi rijista da shi yana son ya ga motsin wannan POS aƙalla sau goma a rana don ya tabbatar da yana aiki. Wannan ba tare da ya kula da yawan kudin da zasu shiga ko zasu fita ba ta hanyar wannan POS din.

v- Zai biya kudin hayar shago da wutar lantarki da kudin data da yake amfani da ita don hawa kan intanet ko kuɗin cajin waya, da sauransu.

6- Mafi girman ayyukan da masu shagunan POS suke yi guda biyu ne:

a- Za su bayar da kuɗi ‘cash’ ga wanda yake so, sai su karɓi ATM card dinsa su ciri daidai kudinsu su tura cikin account dinsu. Misali an biyashi albashi dubu goma (10,000) sai ya zo suka bashi tsurar kudi dubu goma cash, sannan sai ya ba su katinsa mai ɗauke da waɗannan kudade, sai su kwashe daidai kudin da suka bashi daga accout dinsa zuwa nasu.

b- Mutum zai iya kawo kudi kamar dubu goma ya ce a tura masa cikin account dinsa ko kuma a turawa dansa da yake karatu a wata kasa ko a tura a ‘account’ na mahifiyarsa ko dan uwansa ko zai biya kuɗin wutar lantarki, ko kuɗin makaranta da dai sauransu. 

A duk wadannan hidimomi da masu shagon POS suka yi, zasu bukaci a basu wani abu a matsayin ladan aikin da suka yi. A yadda al’adarsu ta gudana a yanzu akwai wani gwargwado na kudi mara yawa da suke karba bisa duk dubu daya ko biyar ko goma ko dari ko miliyan daya da suka bawa mutum ko suka tura masa. Za a iya ba su daga account din mutumin idan da akwai wasu kuɗin a ciki ko ya kawo ladan ya ba su hannu da hannu daga cikin kuɗin da suka bashi.

Za a ci gaba a makon gobe da yardar Allah.

Farfesa Murtala shine Shugaban Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Bayeri, Kano

By ukarofi