Matsin lamba ko son rai: Yadda BBL da bilicin suka zama al’ada a masana’antun nishaɗi

Spread the love

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS 

*Ba a amince da allurar glutathione don sauya launin fata ba – Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka

An samu rahotannin mace-mace da suka danganci BBL fiye da wasu hanyoyin gyaran jiki – ASERF

Mercury na iya haddasa lalacewar ƙoda, matsalar jijiyoyin jiki da kuma illa ga jarirai idan mai ciki na amfani da shi – WHO 

2. Kafafen sada zumunta:

Wasu za su yi mamakin sanyo kafafen sada zumunta cikin wannan layin, saidai da taimakon bayanin da zan yi yanzu za a fahimci inda na dosa. Kafafen sada zumunta ta zama duniya ta biyu da mutane ke shaƙar numfashi a cikinta, kuma hanya ce da aka fi jin ra’ayoyin jama’a da kuma samun karɓuwar fina-finan da ake yi. Abin nufi, fim na tasiri ne idan al’umma sun gamsu da shi, ana sanin gamsurar fim a wannan zamani ta hanyar kafafren sada zumunci. Wannan ya sa jarumai da waɗanda ke neman sharaha ke mayar da kafafen sada zumunci iyayensu wurin biyayya, ta hanyar yawan yaɗa hotunansu don neman yawaba da soyayyar mabiya, wanda hakan zai sa ga jarumai kamfanonin fina-finai su yi ribibinsu. Su kuma masu neman shahara su samu biyan buƙatar da suka yi domin ta.

Shi ya sa za ku ga musamman ma a mata, suna damuwa da ababen da ‘yan kwament suke faɗa kan jiki ko wankansu, a cewar wasu ita ce kasuwarsu. Sau dayawa za ka tarar wani ma yaro ne ƙarami zai aibata wani ɓangare na jikin wata, sai ya samu magoya baya da yawa, kamar misali a faɗi yadda jaruma ta ƙara ƙiba, kuma ƙibar ba ta yi mata kyau ba, zai iya zama dalilin da ita da masu kula da ayyukan sana’ar tata su yanke shawarar ta nemi hanyar rage ƙibar. Wannan na ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ka ke jin wasu jarumai musamman na ƙasashen ƙetare suna ƙorafin rashin damar cin abinda suke ra’ayin ci, sakamakon kula da jikin da masu aiki da su ke yi. Wani lokacin ma har ɗaukar masana ake yi da za su dinga kula da irin abincin da jaruman ke ci, a ƙoƙarin ganin ba ta yi ƙibar da ba a so ta yi ba, ko cin wani abu da zai taɓa kyan fatarta ko makamantansu. (A nan muka dasa aya a makon da ya wuce)

Ko kuma irin wannan zamani na sha’awar diri, mata da dama ana ƙin kallon fina-finasu don kamaninsu, don haka duk iya fim ɗinta sai kaga tana yin baya. Akwai wadda albarkacin dirinta sai a yi ta saka ta a fim tun ba ta iya ba har ta ƙware. Wannan sau da dama ya jefa jarumai marar hangen nesa faɗawa duniyar BBL ko bilis.

Sai kuma matsala ta kwatanta kai da wasu da ke samun gindin zama a kafafen sada zumunta. Kin ɗora hoto, wata can ta ɗora, ke je kinga yadda mutane ke giɗaɗa halittar ta wadda ke ba ki da irinta, sai ki ji kin gaza. Kamar yadda masana ilimin halayyar ɗan adam suka faɗa, kwatanta kai da wasu kan jawo rashin gamsuwa da taka halitta, wadda hakan ke iye kaiwa ga yanke shawarar neman ƙari ta hanyar da ba ta dace ba.

3. Gasa a masana’antar fim:

A harkar fim samun aiki na dogara ne da yadda jaruma ta iya taka rawa a bayan fage, kamar yadda muka faɗa a baya, gasar ba ta tsaya a iya su matan ba, wanda hakan sababben abu ne a tsakanin mata, abin ya yi tsalle zuwa ga su masu bayar da aikin. Sau da dama mata kan yi iya iyawarsu a sana’ar, kuma su masu shirya fim ɗin sun san idan ƙwarewa ake nema su ne kan gaba, amma saboda ba su da abinda ake so ta fuskar kyau sai kaga an ajiye su a gefe, wannan ke sa su yi duba ga waɗanda ake ɗauka suga me suka fi, ta hakan ne za su fara tunanin yadda za su yi su mallaki abinda ake so.

Idan za mu waiwaye wasu matan kamar mawaƙa, nasu lamarin ya sha bamban domin su sun riga sun kai inda saidai a kula masu da kansu, ba za a iya hana su yin waƙa don kamaninsu ba, saidai da yawansu kan zaɓi sauya launin fatarsu ko ƙarin jikinsu don samun ƙarin tagomashi. Hakan wata ɗabi’a ce da ba ɓoyayya ba a tsakanin manyan mawaƙan duniya musamman ma na ƙasashen waje, kasancewar da yawansu sun bayana sun yi kuma suna alfahari da abinda suka yi.

Kasancewar duniya ta juya kan bayyana tsiraici a matsayin wayewa, don haka ba wadda take tashe da yawan masoya matuƙar bata bayyana jikinta ba, kodayake a yanzu fim ɗin gaba ɗaya ya zama na bayyana tsiraici daga gida har ƙasashen waje da suka daɗe suna yin hakan, wannan bayyana tsiraici kuwa zai bayyana abinda ki ke da shi, wanda ta nan ne duniya za ta yi amfani da buƙatarta ta yaba maki ko ta aibata ki.

4. Neman kuɗin shiga ta hanyar talla:

Daya daga cikin romon shahara akwai damar samun tallace-tallace daga kamfafoni wanda hakan na nufin samun wadatattun kuɗi. To suma a wannan ɓangare ba iya shahara suke buƙata ba, suna buƙatar kyakyawan jiki da fata mai kyau don samun tagomashin abinda suka shigar kasuwa. Sau da yawa kuwa wasu kamfanoni suna buƙatar mace mai kyau don nuna inganci da tasirin kayansu, kamar masu tallata kayan gyaran jiki ko na kwalliya.

Binciken masana halayar ɗan adam da ma wasu likitoci sun bayyana ɗaya daga cikin dalilin da ke sa BBL da bilis ƙarin tagomashi akwai yadda jama’a suke kallon mace mai farar fata ko mai diri a fuskar tallace-tallace, ba wai a iya maza ba, har matan. Sau da yawa mace kan kaunace wani abu da ta ga tallan shi don kawai matar da ta yi tallar, musamman ma a ɓanagaren kayan ƙawa.

Bari mu waiwaye masana don jin irin batutuwan da suka yi kan wannan ɗabi’a ta BBL da kuma bilis. 

Shin me masana lafiya suka faɗa game da BBL?

Masu tiyatar gyaran jiki sun sha bayyana cewa: “Tiyatar ƙara girman mazaunai na daga cikin hanyoyin gyaran jiki da ke da haɗari idan ba a yi ta a hannun ƙwararre ba.”

Haka kuma wasu ƙungiyoyin likitoci sun jaddada cewa: “Haɗarin BBL ya fi yawa idan aka kwatanta da wasu hanyoyin gyaran jiki, musamman idan kitse ya shiga cikin manyan jijiyoyin jini.”

Sannan kuma sun yi gargaɗin cewa: “Mutane da dama na yanke shawarar yin tiyata ne bisa sha’awa ko tasirin hotunan kafafen sada zumunta, ba tare da cikakken binciken lafiyarsu ba.”

Idan mun koma ɓangaren bilis kuwa, nan ma duk kanwar ja ce, domin akwai tarin hatsari a cikin wannan ɗabi’a ta sauya launin fata waɗanda masana lafiya suka jima suna gargadi kansa.

ƙungiyoyin lafiya sun sha fitar da sanarwa cewa: “Amfani da sinadarai masu rage launin fata na iya haddasa lalacewar fata ta dindindin.”

Masana ilimin fata sun kuma ce: “Wasu man bilis na ɗauke da sinadarai masu guba da ka iya shiga jini su lalata hanta ko ƙoda.”

Haka kuma, “Sauya launin fata ba ya sauya tsarin rayuwa ko ƙara wa mutum ƙima; sau da yawa yana jefa mai ita ne cikin sabbin matsaloli,” inji masana. 

Masana halayyar ɗan adam sun ce: “Matsin lambar kyan gani a kafafen sada zumunta na haifar da rashin gamsuwa da jiki, musamman a tsakanin mata masu shuhura.”

ƙungiyar likitocin gyaran jiki ta Amurka, wato American Society of Plastic Surgeons ta bayyana cewa: “Tiyatar BBL na daga cikin hanyoyin gyaran jiki da suka fi ƙaruwa a duniya, amma tana buƙatar ƙwararrun likitoci da tsauraran ƙa’idojin tsaro.”

Sun jaddada cewa yin aikin a cibiyar da ba ta cika ka’ida ba na ƙara haɗarin matsaloli kamar toshewar jijiyoyin jini.

Wata gidauniya ta bincike mai suna Aesthetic Surgery Education and Research Foundation ta taɓa gargaɗin cewa: “An samu rahotannin mace-mace da suka danganci BBL fiye da wasu hanyoyin gyaran jiki, musamman idan kitse ya shiga cikin jini.”

Saboda haka suka ba da shawarar a taƙaita yadda ake zuba kitse da kuma tabbatar da ana yin sa a matakin da ya dace a cikin tsoka, ba a yi zurfi ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya, wato WHO kuwa ta yi gargaɗi kan amfani da sinadarai masu ɗauke da mercury a man sauya fata, inda take cewa: “Mercury na iya haddasa lalacewar ƙoda, matsalar jijiyoyin jiki da kuma illa ga jarirai idan mai ciki na amfani da shi.”

Hukumar kula da muhalli ta Majalisar ɗinkin Duniya, wato United Nations Enɓironment Programme ta bayyana cewa: “Yaɗuwar kayayyakin sauya fata masu ɗauke da mercury babbar barazana ce ga lafiyar jama’a, musamman a ƙasashen da ba su da tsauraran duba kaya.”

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka, wato FDA ta yi bayanin cewa: “Ba a amince da allurar glutathione domin sauya launin fata ba, kuma ba a tabbatar da amincinta ba.”

Sun gargaɗi jama’a da su guji kayayyakin da ba su da rajista ko cikakken bayani kan sinadaran da ke ciki.

By ukarofi