Buɗe bakin Ramadan: Sanata Wadada ya baƙunci ƙungiyar ALGON ta Nasarawa

Spread the love

DAGA JOHN DOGO WADA a Keffi

Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattawa ta tarayya sanata Ahmed Aliyu Wadada ya baƙunci shugabannin ƙananan hukumonin jihar Nasarawa a ƙarƙashin ƙungiyar ALGON da masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC mai ci a jihar don cin abincin buɗe baki na azumin watan Ramadan.

Zaman buɗe bakin an gudanar da shine a gidan sanatan da ke GRA a birnin Keffi. Da yake jawabi jim kaɗan bayan buɗe bakin, Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya gode wa duka baƙin nasa musammam shugabannin ƙananan hukumonin dangane da amsa gayyatarsa da yace suka yi cikin lokaci duk da gayyatar ta zo a ƙurerren lokaci.

Ya kuma ja hankalin su da al’ummar jihar baki ɗaya su zauna lafiya da son juna da kuma haƙuri da juna inda ya jaddada cewa idan suna samun rashin jituwa a tsakanin su a ko yaushe, baƙi daga waje za su zo su mallaki ɗimbin arziki da wadata da Allah ya yi wa jihar.

Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya ƙara da cewa yana da kyawawan shiryeshirye da manufofi da dama wa jihar ta Nasarawa idan Allah ya bashi damar ya gaji gwamna Abdullahi Sule a shekara mai zuwa, inda yace tabbas zai ɗora ne daga inda mai girma gwamna Abdullahi Sule zai tsaya a kyawawan ayyukan cigaba da ya ke gudanarwa yanzu a jihar.

Har Ila yau sanata Ahmed Aliyu Wadada ya kuma yi amfani da damar inda ya bayyana cewa shi fa a rayuwar sa na siyasa da sauran harkokinsa na yau da kullum baya gaba da kowa kuma baya gasa da kowa maimakon haka abinda yake yi shine baje kolin ayyukan cigaban da ya daɗe yana yi wa al’umma baki ɗaya ba tare da numa banbancin siyasa, addini ko ƙabila ba.
Daga nan sai Sanatan ya yaba wa gwamna Abdullahi Sule game da ire-iren ayyukan cigaba da gwamnatinsa ke cigaba da gudanarwa a duka fannonin rayuwa a jihar inda yace tabbas gwamnan ya cancanci yabo, kana tarihi ba zai taba mantawa da waɗannan gagaruman gudumawa da yake bayarwa ba har bayan ya bar ofishin gwamnan.

Tun farko da yake jawabi a madadin shugaban jam’iyar APC, mataimakin shugaban Hon. Jatau Kunda ya yaba wa kyawawan halayya irin na Sanata Ahmed Aliyu Wadada inda yace tabbas a kullum abinda ke zuciyar Sanatan shine haɗa kan al’ummar jihar baki ɗaya.

Shi yasa a cewar sa bai yi mamakin gayyatar Sanatan don buɗe bakin watan Ramadan din ba inda ya ƙara da cewa tabbas sanatan zai samu lada na musammam daga wurin Ubangiji dangane da wannan matakin da ya ɗauka domin a cewarsa hakan ma wani ibada ne na musammam da ke jawo sakayya na musammam daga wurin Allah, domin duk wanda ya ciyar da al’umma buɗe bakin a wannan wata mai rahama ta azumi ladan sa na daban ne.
A ƙarshe shima da yake jawabin godiya, shugaban ƙungiyar ƙananan hukumonin jihar ta Nasarawa wato ALGON a turance wanda shine kuma shugaban ƙaramar hukumar Akwanga wato Hon. Safiyanu Isah Andaha ya miƙa godiyarsa na musamman a madadin shugabanni da sauran al’umma baƙi daga Sanata Wadada game da karamcin, inda ya kuma buƙaci shugabanni a duka matakai su yi koyi da kyawawan ɗabi’u irin na sanatan don cigaban jihar baki ɗaya kana ya ƙara da cewa a nasu ɓangaren za su yi aiki da duka shawarwari da nasiha da suka ji daga wurinbsanatan.

By ukarofi